EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Daga Waƙoƙin mu
Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kori sama da ma’aikatanta 40 bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma almundahana cikin shekaru uku da suka gabata.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wata ganawar manema labarai da aka shirya domin bikin cikar sa shekaru uku a matsayin shugaban hukumar.
Ya ce matakan ladabtarwar na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da gaskiya da riƙon amana da bin ƙa’ida a cikin ma’aikatanta, tare da ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa. Ya kuma bayyana cewa kusan jami’an EFCC biyar ne a halin yanzu ke fuskantar shari’a kan zargin aikata rashawa.
Ya sake jaddada aniyar EFCC na tabbatar da ƙwarewa da gaskiya da riƙon amana wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka shafi kuɗaɗe.
Ya ce: “A cikin shekaru biyu da rabi zuwa uku da na yi ina aiki, na nemi a kori ma’aikata sama da 40 bisa dalilan cin hanci da rashawa da kuma almundahana ta kuɗi. Fiye da biyar daga cikinsu kuma a halin yanzu ana binciken su.”
Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
A cewarsa, wasu daga cikin jami’an da abin ya shafa tuni suna gaban kotu, yayin da ake shirya takardun shari’a da fayilolin wasu domin gurfanar da su.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
ÁOlukoyede ya ce hukumar ba za ta kare ko ta yi wa ma’aikatanta garkuwa daga fuskantar shari’a ba idan aka zarge su da aikata cin hanci da rashawa. Ya bayyana cewa idan EFCC tana bincike da gurfanar da mutanen da ba ma’aikatan hukumar ba kan cin hanci da rashawa, to dole jami’anta su ma su fuskanci doka idan suka aikata irin wannan laifi.
Shugaban EFCC ya ce matakan ladabtarwar na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa jami’an hukumar suna riƙe da irin matakin gaskiya da amana da ake sa ran sauran ’yan Najeriya za su kasance da shi.
“Dole ne ku tabbatar hannayenku suna da tsabta. Ba za ku iya yaƙi da cin hanci da rashawa ba alhali hannayenku sun gurɓata da ayyukan rashawa,” in ji shi.
Olukoyede ya kuma sanar da cewa hukumar ta sauya sunan tsohuwar Sashen Harkokin Cikin Gida (Internal Affairs Department) zuwa Sashen Da’a da Gaskiya (Department of Ethics and Integrity), domin ƙarfafa ladabtarwa a cikin hukumar da kuma inganta ɗabi’a da gaskiya tsakanin jami’an EFCC.
Hukumar ta kuma ƙaddamar da manufar karɓar kyaututtuka domin inganta gaskiya da kuma hana rikicin moriyar kai tsakanin jami’anta. Ya ce a ƙarƙashin sabuwar manufar, za a bukaci ma’aikatan EFCC su bayyana duk wata kyauta da suka samu wadda ta haura wani adadi da aka kayyade, ciki har da kyaututtukan da suka samu daga abokai da ’yan uwa a Najeriya da ƙasashen waje.
Olukoyede ya ce hukumar za ta kuma kayyade nau’ikan kyaututtukan da jami’anta za su iya karɓa, tare da buƙatar su bayyana tushen kuɗin shigarsu da kuma yadda rayuwarsu take.
Ya yi kira da a ƙara yin gyare-gyaren hukumomi da inganta manufofi domin magance cin hanci da rashawa, yana mai cewa amfani da jami’an tsaro da hukumomin tilasta bin doka kaɗai ba zai kawo ƙarshen laifukan da suka shafi kuɗi ba.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Sarkin Noma Nadabo Chiromawa Ya Kubuta, Yana tare da Iyalan Sa
A cewarsa, hanya mafi inganci wajen yaƙi da laifukan kuɗi ita ce samar da ingantattun manufofi da gyare-gyaren hukumomi da za su toshe hanyoyin da ake amfani da su wajen satar kuɗaɗen gwamnati.
Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula su ƙara ƙarfafa rawar da suke takawa wajen sa ido da bibiyar ayyukan gwamnati a yaƙi da cin hanci da rashawa.




























