Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha

Daga Wakilin mu

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Talata, 1 ga Satumba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bai wa mazauna jihar damar gudanar da bikin Takutaha.

Bikin Takutaha wata muhimmiyar al’ada ce ta addini da ake gudanarwa a duk shekara domin tunawa da zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabin Muhammadu (SAW).

Sanarwa ta fito daga Ofishin Ma’aikata na jihar Kano wadda Babban Sakatare a ma’aikatar Alhaji Abba A. Danguguwa, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Hajiya Bilkisu Maimota.

Mutane 16 Gini Ya Faɗawa A Unguwar Dandishe A Kano

Sanarwar ta ce ranar hutun ta yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1448 bayan hijira, inda ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da ayyana ranar a matsayin hutu.

Gwamnatin ta bayyana Takutaha a matsayin muhimmiyar al’ada mai alaƙa da addini da tarihi, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga al’ummar jihar Kano tare da kasancewa wani ɓangare na tarihin Musulunci na jihar.

Ta buƙaci ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da ranar wajen addu’o’i da neman gafara, tare da roƙon Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnati Kano Ta Ayyana Yaƙi da Dillalan Bogi, Ta  Hana Duk Wata Hada-Hadar ƙasa a Filayen Makarantu Da Asibitoci Mallakinta”

Sanarwar ta umurci shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su tabbatar da bin umarnin, sai dai sanarwar ta ce ma’aikatan da ke kula da muhimman ayyuka za su ci gaba da aiki kamar yadda tsarin hukumominsu ya tanadar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...