Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Daga Wakilin mu
Jajircewa da ƙwazon da wani jami’in Hukumar KAROTA, Naziru Alhassan Madobi, ya nuna ya kai ga gano wata mota da aka sace daga wani wurin taro (Event Centre) da ke kan titin Lawan Danbazau, kusa da tsohon gidan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) a cikin birnin Kano.
A sanarwar manema labarai da ya sanyawa hannu, Mai magana da yawun Hukumar KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya nunar cewa Lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis, inda wasu mutane masu kishin ƙasa da ke aiki a matsayin masu sayar da mai a gidan man Aliko da ke kusa da wurin taron suka fara sanar da abin da ke faruwa.
Jami’in KAROTA, Naziru Alhassan Madobi, wanda ya kammala aikinsa a ranar, ya tsaya a gidan man Aliko. Da ya lura da wani yanayi da ba na al’ada ba, sai ya tambayi ma’aikatan gidan man abin da ke faruwa. Suka shaida masa cewa wani mutum na ƙoƙarin satar wata mota, amma kafin su ankara ya kunna motar tare da tserewa cikin matsanancin gudu.
A nan ne Naziru Alhassan Madobi ya fara bin motar, inda aka bi ta ta Gandun Albasa, gidan Bashir Tofa, hanyar Jami’ar Baba Ahmed, Sharada, gidan man A.A. Rano, sannan aka dawo ta hanyar Kwalejin Rumfa da ke Dan Agundi. A yayin gudun, ɓarawon ya buge mutane da dama da ke kan hanya, amma hakan bai sa jami’in KAROTA ya daina binsa ba har sai da ya isa makabartar Tukuntawa, inda motar ta yi karo da wata magudanar ruwa.
Read also: Zamu Rinƙa Ciyar da Ma’aikatan KAROTA Gaba A Kan Lokaci, In Ji MD Faisal Mahmoud
A nan ne, tare da taimakon taron jama’a, aka kama wanda ake zargin. Jama’ar sun yi yunƙurin hukunta shi da kansu, amma jajirtaccen jami’in KAROTA ya shiga tsakani ya ceci rayuwarsa. Daga nan sai ya sanar da Rundunar ‘Yan Sandan Sharada, inda aka kama wanda ake zargin domin ci gaba da bincike.
Da yake ƙarin haske kan kama wanda ake zargin da kuma binciken da aka gudanar, Naziru Madobi ya bayyana cewa binciken ‘yan sanda ya gano cewa wanda ake zargin ɗan asalin Jihar Bauchi ne, kuma yana cikin wata ƙungiyar masu satar motoci. Wannan binciken ya kuma kai ga gano wasu motoci da dama da aka sace waɗanda ƙungiyar ke da hannu a cikinsu.
Da yake tsokaci kan wannan bajinta da jajircewa da Naziru Madobi ya nuna, Manajan Daraktan Hukumar KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya yaba masa matuƙa, tare da alƙawarin cewa hukumar za ta ci gaba da karrama ma’aikatan da suka nuna ƙwazo, jajircewa da nagarta wajen gudanar da ayyukansu.
Shugaban KAROTA ya kuma buƙaci sauran jami’an hukumar da su yi koyi da kyakkyawan misalin da Naziru Alhassan Madobi ya nuna wajen gudanar da aikinsu.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
A nasa ɓangaren, mijin mai motar da aka sace, Hon. Habibu Baballe Ila, ya yaba da kishin ƙasa da sadaukarwar da Naziru Madobi ya nuna. Haka kuma ya jinjinawa Manajan Daraktan KAROTA da daukacin shugabannin hukumar bisa kyakkyawar tarbiyya da horon da suke bai wa jami’ansu.




























