Hukumar NDLEA ta Gano Maboyar Miyagun Kwayoyi a Karkashin Kasa a Kano
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara
Reshen hukumar NDLEA na jihar Kano ya gano wasu kogona da ramuka na ƙarƙashin ƙasa waɗanda masu sha da sayar da miyagun ƙawayoyi ke amfani da su domin boye kwayoyi a unguwar Rimin Kebe.
Jami’en Hulda da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya sanar da haka, a sakon da ta manema labarai a Kano
Kamar yadda hukumar ta sanar ta ce, a ranar 4 ga watan Mayu, 2026, jami’en Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta Ƙasa reshen jihar Kano suka bankaɗo kogona da aka gina da abubuwan ban mamaki, inda aka samu dabbar kada da magungunan ciwon gwiwa (arthritis), da takardun raba abinci, waɗanda ke nuni da cewa mutane suna rayuwa a cikin gurin.
Haka kuma an gano wasu dogayen ramuka masu zurfi waɗanda ke haɗe da wani babban rami a ƙarƙashin kasa, wanda suke zargin anan miyagun mutane ke buya.
Kwamandan NDLEA na jihar Kano, Dahiru Yahaya Lawal, ya bayyana cewa bayan nazari da kuma amfani da bayyana siri shi ya basu damar bankaɗo wanna guri kuma tuni suka fara rusa wuraren.
Shugaban ya ce hukumar su ba za tai ƙasa a gwiwa ba na bin diddigin masu wannan muguwar sana’a ba, har sai sun share fataucin miyagun ƙwayoyin baki ɗaya a faɗin jihar Kano.
Dahiru Lawal, ya buƙaci daukacin jama’a da su ci gaba da ba su haɗin kai ta hanyar basu bayanan sirri domin kawo karshen muguwar ta’ada.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Kwamishina ‘Yan Sanda Ya Ce Sun Tattara Sunayen Masu Dillacin Ƙwaya A Kano Sama Da 2000
Shugaban ya ce hukumar NDLEA ta yi amfani da wani gagarumin bangare mai suna ‘Operation Sharar Asylum’ wanda manyan Jami’ai ne ke jagorantar wannan sabon shiri domin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a jihar, don haka ya yi kira ga al’umma da su basu haɗin kai domin cimma manufa.




























