Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa

Hon. Murtala Suke Garo
Hon. Murtala Suke Garo

Gwamna Abba ya miƙa sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama mataimakin Sa

Daga Sunusi K/Naisa

A wani mataki na bin ƙa’ida ga kundin tsarin mulkin ƙasa, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Alhaji Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da amincewa ya zama Mataimakin Gwamnan jihar Kano.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu kuma ya aikowa manema labarai.

Matakin ya yi daidai da tanadin sashi na 191(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), wanda ya bai wa gwamna ikon naɗa mataimakin gwamna idan an sami gurbin.

Idan za a iya tunawa ta  tsohon Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi murabus don ƙashin kansa a ranar 27 ga Maris, 2026, wanda hakan shi haifar da dogon tsako inda ofishin Mataimakin gwamna ya zama babu kowa. Hakan ya sa zawarawa suka yi wa ofishin tsinke domin ganin gwamna ya bayar da sunan ɗaya daga cikin su.

Ga wasu Labarun:

Canja Jam’iyya a Siyasar Kano Ya Zo a Kan Lokaci, Kuma Muniface Mai Kyau– Inuwa Waya

Wazirin Ningi Ya Yi Murabus, Sakamakon Tsoma Siyasa a Harkokin Masarautar Ningi

Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, Gwamnan ya bukaci Majalisar Dokokin Jihar ta amince da  naɗi Murtala Garo ya zama namba biyu a jihar Kano.

Ɗan shekaru 48 da haihuwa, Murtala Sule Garo gogaggen ɗan siyasa ne mai fiye da shekaru 20 na kwarewa a mukamai daban-daban.

Murtala ya taɓa zama Sakataren Tsare-tsare na jam’iyya a jiha, Mai bai wa gwamna shawara kan hulɗar gwamnatoci, sannan kuma zababben Shugaban Karamar Hukuma.

Haka kuma ya riƙe mukamin Shugaban ALGON a Kano, ya kuma zama Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, tare da zama ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Masu lura da al’amuran siyasa sun ce wannan naɗi na daga cikin ƙoƙarin ƙara inganta shugabanci da kuma ci gaba da samar da ayyukan more rayuwa ga al’ummar Jihar Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...