Kwamishina ‘Yan Sanda Ya Ce Sun Tattara Sunayen Masu Dillacin Ƙwaya A Kano Sama Da 2000
Daga Sunusi K/ Naisa
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta tattara sunayen fiye da mutum 2,000 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na jihar, kuma tana bin hanyoyin da suka kamata domin tabbatar da sun shiga komar su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da ya yi kan halin tsaro a watanni ukun farkon shekarar 2026.
Ya ce rundunar ta cimma wannan nasara ne ta hanyar inganta tattara bayanan sirri da kuma haɗin kai da al’umma, wanda ya ba su damar gano masu hannu a safarar miyagun ƙwayoyi.
“Mun samu sunayen fiye da mutum 2,000 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, kuma ana ci gaba da tantance su domin ɗaukar matakin da ya dace,” in ji shi.
Read also: DA ƊUMI-ƊUMI: Wasu Fusatattun matasa sun kashe DPO ‘Yan Sanda har lahira a Kano
Nambobin Wayar Kar-Ta-Kwana Daga Hukumar Yan Sandan Jihar Kano
Ibrahim Bakori ya kuma ce an samu raguwar aikata laifuka a Kano a cikin watanni ukun farkon shekarar nan, yana mai danganta hakan da sabbin dabarun tsaro da rundunar ta bullo da su.
A cewarsa, matakan sun haɗa da kai samame na musamman da kuma amfani da fasaha wajen bin diddigin masu aikata laifuka ta hanyar amfani da sahihan bayanai.
Kwamishinan ya ce wani shiri na musamman mai suna Operation Kukan Kura ya taimaka wajen rage ayyukan daba da fashin waya a jihar.
Haka kuma rundunar ta kama mutane da dama da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma laifukan intanet.
Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Bakori, ya kuma yaba wa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar. Sai dai ya ce har yanzu akwai ƙalubalen tsaro da ke buƙatar ƙarin ƙoƙari, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa a jihar.




























