Sama da ‘Yan Bindiga 150 Sun Nutse a Hatsarin kwale-kwale a Kogin Sokoto
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Gami Da Garkuwa Da Wasu A Kano
Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 150 da ake zargin ‘yan bindiga ne sun nutse a cikin ruwa a yankin Sabon Gida da ke Jihar Sokoto.
An ce ‘yan bindigar sun nutse ne a yammacin ranar Asabar bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da su yana tsallaka wani babban ruwa ya kife, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dukkanin waɗanda ke cikinsa.
Ana kallon wannan lamari a matsayin babbar koma baya ga ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma.
A cewar rahotannin farko da aka fitar ranar Lahadi ta hannun Zagazola Makama, wani ƙwararre da ke nazari da bayar da rahotonnin kan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, ‘yan bindigar na tafiya ne cikin wani babban kwale-kwale da ɗauke da mutane da yawa. Rahoton ya ce kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar ruwa, inda ya hallaka dukkanin mutanen a cikin tsakiyar ruwa.
Read also: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono
Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Makama, wanda ya wallafa bayanin ta shafinsa na X (wanda a da ake kira Twitter), ya ce mutuwar ‘yan bindigar da a ke Zargin ba wanda ya tsira da ransa ya faru ne sakamakon rashin iya ninƙaya (iyo) da dama daga cikin mutanen, musamman ganin cewa suna ɗauke da manyan makamai.
Ya ce, “Bayanan farko sun nuna cewa da dama daga cikinsu ba su iya iyo ba, wanda ya jawo asarar rayukan nasu. Rahotannin farko sun tabbatar babu wanda ya tsira daga hatsarin.”
Yankin Sabon Gida, wanda ke kusa da iyakokin Jihar Sokoto, ya daɗe yana zama hanyar wucewa ga miyagun mutane da ke zirga-zirga tsakanin maboyarsu da ke cikin dazuzzuka.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto da kuma Hedikwatar Tsaro ta Kasa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba domin tabbatar da gano gawarwaki ko kuma haƙiƙanin mutanen da hatsarin ya rutsa da su ba.
Read also: Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI
Sai dai majiyoyin cikin gida sun ce akwai yiwuwar ‘yan bindigar na guduwa ne daga hare-haren sojoji da ake ci gaba da kai wa a wasu ƙananan hukumomi maƙwabta kafin su gamu da wannan ajalinsu.



























