Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: Gobara : Kasuwar Ƴan Katako A Kano Ta Kama da Wuta
Wata mahaukaciyar gobara ta lalata sassan gidaje uku tare da wani wurin da ake ajiye na’urar rarraba wutar lantarki (transformer) a yankin Gaida kusa da Fatima Bread, a Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
A cewar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, lamarin ya faru ne a ranar Talata, 17 ga Maris, 2026, da misalin karfe 11:05 na safe, lokacin da sashen bayar da agajin gaggawa ya samu kiran neman dauki daga wani mazaunin yankin mai suna Aminu Bello.
Jami’an kashe gobara daga Shelkwatar hukumar, tare da tawaga daga tashoshin kashe gobara na Sharada da Rijiyar Zaki, sun kai ɗauki cikin gaggawa zuwa wurin domin shawo kan gobarar.
Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Read also: Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce da isarsu wurin, jami’anta sun tarar da wani fili mai fadin kusan kafa 50 da 50, wanda ake amfani da shi a matsayin wurin da aka girke na’urar rarraba wutar lantarki, gaba daya ya kama da wuta.
Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama
Gobarar ta bazu cikin gaggawa zuwa gine-ginen da ke kusa, inda ta shafi gidajen zama uku masu girma dabam-dabam. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya yi tsanani, inda wutar ta cinye sassan gine-ginen kafin jami’an agajin gaggawa su samu nasarar shawo kanta.
Jami’ai sun tabbatar da cewa ginin farko, wanda karamin gida ne na zama, ya fi shan mummunar barna, yayin da gini na biyu, mai bene ɗaya, ya samu babbar illa, musamman a saman benen.
Gini na uku, wanda shi ma gidan zama ne, shi ma gobarar ta yi masa barna.
Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga tartsatsin wutar lantarki.
Read also: “Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
Da yake jawabi kan lamarin, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Sani Anas, ya bukaci mazauna yankin da su riƙa ba da muhimmanci ga matakan kariya.
Hukumomi sun ce ba a samu asarar rai ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano cikakken girman barnar da gobarar ta haddasa.



























