Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama

Shugaban Ƙasa Tinubu
Shugaban Ƙasa Tinubu

Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama

Daga Sunusi K/Naisa 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince  ranakun Alhamis 19 ga Maris da Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin hutu domin bikin sallah karama, wanda ke nuna kawo ƙarshen watan azumin Ramadan.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, Ministan ya kuma taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.

Tunji ya bukaci Musulmi da su cigaba da riƙo da kyawawan ɗabi’u kamar kaunar juna, karamci, zaman lafiya, haƙuri da kuma sadaukarwa, waɗanda su ka koya a cikin watan Ramadan.

Haka kuma ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen yin addu’o’i domin ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Tsaro: Hukumar Yan sanda ta Haramta Yin Wasan Tashe

Ministan ya kuma shawarci al’umma da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin natsuwa tare da taimaka wa marasa galihu.

Saudiyya ta Sanar da Ganin Watan Ramadan

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin ‘yan Najeriya baki ɗaya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...