Ana Zargin Batagarin Matasa Da Bankawa Dubban Kaburbura Wuta A Makabartar Turum Dake Bauchi
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: An Nemi a Gyara Auran Matasa Da Sukai Aure Akan Sadaki ₦3000, A Maimakon Dauri
A ƙarshen makon da ya gabata an samu tashin wutar a maƙabartar Tudun-Salmanu dake Gurin a jihar Bauchi, wadda tai sanadiyar konewar dubban ƙabarbura a wannan maƙwabtaka.
Maƙwabtan maƙabartar sun ce ce ya zama al’ada duk shekara bata-garin matasan kan kuna wuta a maƙabartar, kuma haka ma bana suka sake aiwatar wa da tsakiyar ranar Lahadi.
Read also: ICPC Ta Kama Dan Jaridar Bisa Zargin Damfara Ta Naira Miliyoyin 14
Maƙwabtan, sun bayyana cewa ana sako wutar daga gefen unguwar Madina da Makara huta da ke gabas da kudancin makabartar.
Jami’an Hukumar kashe gobara ta jiha da ta Tarayya da ke Bauchi sun kokarta wajen kashe wutar da taimakon al’ummar unguwa.
Amma daga bisani batagarin yaran unguwar da ake zaton sune ke sa wutar sun nemi mayar da lamarin ya koma tarzoma, a inda suka fara jifar Yan kwana-kwanan kafin daga bisani matasan unguwa suka ci karfin su suka wargaza su. Suma jami’an kwana-kwanan suka gayyato Yan sanda don kawo musu ɗauki.
Read also: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Ƙaddamar da Hasken Solar a Dajin Yankari
Ma’aikatan Kashe gobara sun bayyana cewa idan ba a ja kunnen yaran unguwar ba kan cin zarafin su, to nan gaba idan aka sa wutar ko an gayyato su baza su zo ba don kare martaba da lafiyar su.
Yawanci ana sa wutar ne tsakiyar rana da zaton masu Shaye Shaye ko farautar gafiyoyi da kuregi ke sa wutar da yawanci ke cinye akasarin filayen da kaburburan bayin Allah ke kwance.
A lokacin da lamarin ke faruwa ba a iya shiga da motar kashe gobara saboda akasarin kaburburan suna fashe, saiko su watsa ruwa daga inda suka samu hali.



























