Wazirin Ningi Ya Yi Murabus, Sakamakon Tsoma Siyasa a Harkokin Masarautar Ningi
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kaɗu Matuƙa Da Rasuwar Ƴan Jarida Sakamakon Hatsarin Mota
Read also: Maniyata aikin Umara daga Indiya mutum 42 sun mutu sakamakon hatsarin mota a Saudia
Wazirin Ningi, Ambasada Alhaji Shuaibu Ahmed Adamu (FCA, FCCA), tsohon dan takarar Gwamna a jamiyyar NNPP ya ajiye mukaminsa na Wazirin Ningi, Babban Dan Majalisa (Senior Councillor), da kuma Shugaban Masu Zaɓen Sarki, a masarautar Ningi.
Ya bayyana haka ne sakamakon abin da ya kira ana tsoma siyasa a cikin harkokin tafiyar da Masarautar ta Ningi.
A cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Janairu, 2026, wadda ya aikewa Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Muhammad Danyaya, tsohon Wazirin ya ce ya yanke shawarar ne bayan dogon nazari da tunani kan yadda siyasa ke ƙoƙarin shafar tsarin gudanarwar gargajiyar masarautar, kuma hakan a ganinsa bai dace ba.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse
Ya kara da cewa ya shafe kusan shekaru huɗu yana rike da mukamin Wazirin Ningi, inda ya ce ya yi aiki da gaskiya, adalci da biyayya ga al’adu da dokokin masarauta, Kuma ya gode da wannan dama da aka ba shi.
Sai ko ya nuna damuwarsa kan wani umarni daga Gwamnatin Jihar Bauchi da ya nemi a rage darajar mukaminsa na Shugaban Masu zaɓen Sarki, wanda ya ce ba sakamakon bukatar majalisar masarauta ba ne, illa tsangwama daga wasu ‘yan siyasa da ya ke ganin hakan ba zai amfanar ba.
A cewarsa, amincewa da wannan sauyi zai zama tamkar ya yarda a saka siyasa cikin tsarin gargajiyar masarauta, abin da ya ce ya saba wa rantsuwar da ya dauka na kare martabar al’adu da dokokin masarautar Ningi.
Ambasada Shuaibu Ahmed ya gode wa tsohon Sarkin Ningi, marigayi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, da kuma Sarkin Ningi mai ci, bisa damar da aka ba shi na yi wa masarauta hidima.
Haka kuma ya nuna godiyarsa ga daukacin al’ummar Ningi bisa goyon baya da amincewar da suka ba shi lokacin da yake bisa sarautar da kuma bayan saukarsa.
Rigimar Masarautar Kano Na Daf Da Zama Tarihi, In Ji Kwamishina Waiya
Ya jaddada cewa duk da murabus din, zai ci gaba da kasancewa mai kishin masarauta da al’ummar Ningi tare da bayar da dukkan gudummowar da ta dace don ci gaban yankin.




























