Rikicin Manoma da Makiyaya Yai Sanadiyar Rasa Rayukan Ƴansanda 5 da Ɗanagaji A Bauchi
Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi
Read also: HISBAH A BAUCHI TA HUKUNTA MATASAN DA SUKA DAURA AUREN SADAKIN N3000
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun abkawa jami’an ‘yan sanda a Garin Sabon Sara dake karamar hukumar Darazo jihar Bauchi a ranar lahadi da ta gabata a inda suka kashe jami’ai biyar daga cikin ‘yansandan.
Maharan sun fito da manyan Bíndigogí sun kashe ‘yan sandan biyar nan take kuma suka raunata mutum biyu a yayin musayar wuta a lokacin da suka je don raba rikicin makiyaya da manoma da ke faruwa a dukkanin shekara irin wannan.
Read also: YAN BANGA DA MUTANE 19 SUN RASU A YAYIN ARANGAMA DA YAN BINDIGA A YANKIN DA GWAMNAN BAUCHI YA FITO
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Bauchi SP Mohammed Ahmed Wakil shine ya bayyana haka cikin sanarwa da ya turawa manema labarai.
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono
Ya bayyana sunayen ‘yansandan da suka a lokacin gudanar da aikin waɗanda suka haɗar da DSP Ahmad Muhammad daga sashin (SID) da ASP Mustapha Muhammad daga (10 PMF) da Inspector Amarhel Yunusa daga (10 PMF) da Inspector Idris Ahmed (10 PMF) sai kuma Corporal Isah Muazu daga (AKU).
Haka kuma sanarwar ta ce Ins. Isa Musa da Ins. Yusuf Gambo sune suka samu raunuka a yayin kwantar da rikicin wanda a halin yanzu suke karɓar magani a asibiti.
Tuni dai kwamishinan Yan sanda Sani Omolarin Aliyu ya tura wasu dakarun ‘yan sanda zuwa yankin don farauto ‘yan bindigar da aka ce sun jima suna addabar mutane a waɗannan garuruwa.
Sani Omolarin ya ƙara da cewa a shirye rundunar take na ganin ta kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki don gabatar da su a gaban kotu.
Kwamishina ya ce Baturen ‘Yan sanda na Darazo SP Auwalu Ilu ya sanar da rundunar halin rashin tsaron da ake fiskanta a garin na sabon Sara na rikicin manoma da makiyaya, shine aka tura jami’an ‘yan sanda na musamman don shawo Kan lamarin amma suka yi wa ‘yan sandan kwanton ɓauna suka kashe su.
A wani makamancin labarin kuma wasu maharan sun kai wani farmaki kan wani Dan agajin Izala mai suna Malam Mohammed Bakoshi inda suka hallakashi har lahira a inda su kuma suka gudu.
Lamarin ya faru ne a yankin Zalau da ke ƙaramar hukumar Toro, a ranar Asabar da ta gabata. Ya zuwa wannan lokacin da Wakilinmu ya aiko da rahoton, rundunar ‘yan sanda ta Bauchi ta sake tura jami’anta zuwa yankin don farauto maharan.
Read also: AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI
Ƙaramar Ministar Abuja, Dr. Mariya Bunkure ta Faranta Zukatan Tsofaffin Abokan Aikinta Na AKTH
Idan za a tuna yankuna a jihar Bauchi sun yi kaurin suna game da faɗa tsakanin Manoma da makiyaya musamman a lokutan girbin amfanin gona.



























