Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Rashin aikin yi: Ɗalibai a Najeriya sun fara sauya tunani daga karatu zuwa ilimin koyan sana’a – Dr. Auwal Amba

Dr Auwalu Amba
Dr Auwalu Amba

Rashin aikin yi: Ɗalibai a Najeriya sun fara sauya tunani daga karatu zuwa ilimin koyan sana’a – Dr. Auwal Amba

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Shugaban kwalejin Ilmi da nazarin Shari’a da addinin musulunci ta A.D. Rufai da ke garin Misau Dr. Auwal Ibrahim Amba, ya bayyana damuwa game da yadda dalibai matasa ke kauracewa karatun boko zuwa koyon Sana’a saboda ganin da dama suna kammala karatu basa samun aiki da takardun da suka samu a makarantun zamani.
Dr. Auwal Amba ya bayyana haka ne cikin hirarsa da manema labarai a ofishin sa da ke Misau lokacin da jaridar Alheri ta karrama shi saboda gudunmowa da ya ke bayarwa a fannin ci gaban Ilmi da zamantakewa a Najeriya.
Don haka ya roki shugabannin Najeriya su himmatu wajen ganin sun rage wasu ayyukan gina kasa don a mayar da hankali wajen cike guraban ayyukan da ake da su a makarantu da asibitoci da sauran ma’aikatun Gwamnati.
Ya kara da cewa rashin aiki tsakanin mutanen kasa hatsarine musamnan ga matasa. Hakan ke haifar musu da tunanin aikata miyagun ayyuka da tayar da hankalin mutane, lamarin da ya sa a daidai wannan lokacin ake fiskantar kalubale mai girma game da zaman lafiya da tsaro.

Yadda Laftanar AM Yarima ya tsallake harin ‘yan bindiga
Dr Auwal Amba ya kara da cewa talauci na taka muhimmiyar rawa wajen ruguza rayuwa, don haka yara da ke shiga manyan makarantu basa iya dawainiyar karatun ta yadda an kai lokacin da wanda suke karatun a wasu lokuta basa iya biyan kudin zangon karatu da bai taka kara ya karya ba.
Bayan haka an kai a wasu lokutan za a fara jarrabawa anma sama da rabin dalibai basu yi rijistar zangon karatu ba ala tilas suke barin kowa ya zauna jarrabawa kafin fitar sakamakon a yi rijistar kafin dalibi yaga sakamakon sa.
Yace zuwa wannan lokacin suna bin dalibai da dama kudin makaranta saboda idan an kore su asara ce ga dalibai da makarantar da kasa baki daya.
Shugaban ya bayyana cewa a halin yanzu kyauta suke raba takardar cikewa wato form don neman shiga makarantar amma sun buga guda 3000 a bana har yanzu 480 aka karba don neman shiga wannan makarantar.
Hakan ya nuna akwai matsala sosai saboda yaran a yanzu sun daina sha’awar karatun sun koma neman kudi ta hanyar Sana’a saboda ganin idan sun yi karatu babu aiki.
Haka Kuma wanda Allah ya duba lamarin su aka dauke su aiki kullum suna cikin kukan babu ingancin albashin ko yanayin aiki mai kyau, lamarin da ya sa a kullum ake tafiya yajin aiki har mutum ya gama rayuwar aikin bai hassala komai wa kansa da Iyalan sa ba sai zama cikin wahala.
Bayan haka yaran suna nazarin ganin iyayen su ko mutane da dama sun yi aikin sun kai ritaya basu samu harkokin su ba sai lissafi da zaman jiran tsammani.
Don haka Dr. Auwal Ibrahim Amba ya roki shugabannin Nigeria su dubi lamarin matasa da suka kammala karatu a rika basu aiki don cike guraban da wasu suka bari don a samu ci gaba.
Ya kara da cewa ba makarantar sa kadai ke fiskantar kalubale a wannan fanni ba, saboda ba da jimawa bane hukumar lura da jami’o’in kasa NUC ta fitar da sunayen wasu jami’o’in da ke fama da karancin dalibai kasa da mutane dubu kuma aka bukaci su kara neman dalibai saboda hakan ya saba da dokar hukumar.
Alhaji Auwal Amba ya bayyana cewa cikin shekara takwas da yayi yana jagorantar makarantar da aka fi sani da CLIS Misau sau daya suka kara kudin rijistar shiga makarantar ya kai naira dubu talatin, amma duk da haka suna bin dubban dalibai bashin kudin makaranta sai ran da suka zo karban takardun suke biya.
Amma idan irin wadannan dalibai sun sake tsarin karatu sun dauki wata hanya ta daban a Jamia shike nan basa sake biyo baya don karbar takardun, shike nan sun yi asarar kudin da aka biyo su.
Idan kuma an kore su an hana su zana jarrabawa shima asarace saboda dole a buga takardun kamar yadda aka Saba.
Don haka ya ce manyan makarantu sun shiga tsaka mai wuya saboda ko a kwanakin baya Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya zauna da shugabannin dukkan manyan makarantu na jihar Bauchi ya saurari kukan kowa amma matsalar duk daya ce, Kuma duk bata rasa nasaba da yaran a yanzu sun daina ba karatun muhimmanci saboda ganin moriyar sa raguwa ta ke yi.
Auwal Ibrahim Amba ya kara da cewa ganin girman matsalar da Ilmi ke fiskanta ala tilas suka fito da hanyoyin Sana’a na sarrafa biredi da gidan ruwan Pure water da sauran sana’o’i don samun kudin shiga ta hanyar koyar da koyar da dalibai Sana’a tunda abin da suke so kenan.

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat
Don haka bai gusheba ya gode wa jaridar Alheri Kindness Mai fitowa cikin harshen Hausa da turanci ganin yadda take gudanar da ayyukan ta shekara 13 kuma ta tuna da shi ta karrama shi da lambar yabo saboda kokarin sa kan bunkasa Ilmi da ciyar da Jama’a gaba.
Editan jaridar Alheri ya bayyana cewa sun lura da kokarin Dr. Auwal Ibrahim Amba na hakurin zama da mutane duk da irin kalubale da ya fiskanta tsawon shekara takwas yana jagorantar wannan makarantar.
Don haka jaridar da ma’aikatanta suna masa fatar Alheri da samun ci gaba da nasarar rayuwa a yadda zai Koma aiki bayan ya gama zaman sa na aiki a wannan makarantar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...