Yadda Laftanar AM Yarima ya tsallake harin ‘yan bindiga
Daga Edita
Read also: Sama da ‘Yan Bindiga 150 Sun Nutse a Kogin Sokoto
Rahotanni sun nuna cewa Laftanar Ahmed Yerima ya tsira daga wani yunkurin hallaka shi da yammacin Lahadi, bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi ƙoƙarin kai masa farmaki.
Majiyoyi daga rundunar sojoji sun shaida wa jaridar Vanguard cewa lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Lahadi, lokacin da wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya a cikin motocin Hilux guda biyu suka biyo shi akan hanya a Abuja wajen titin Gadanasko.
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono
Wannan harin ya faru kusan mako guda bayan ta sa-in-sa da ta kaure tsakanin Laftanar Yerima da Ministan Abuja, Nyesom Wike akan ta ƙaddama akan wani katafaran fili na wani babban soji a ƙasar nan.
Read also: Daraktoci 6 Na Ma’aikatar Tsaro Ta Kasa Sun Faɗa Komar Yan Bindiga
Ɗalubai Sun Hallaka Malaminsu A Sanadiyar Chacha
Ministan Abuja na zargin filin da wasun makamantan su an mallaki filin ba bisa ƙa’ida ba.



























