Connect with us

Hi, what are you looking for?

RA'AYI

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA MAI GIRMA ƊAN MAJALISAR TARAYYA, MAZABAR GWALE

Ɗan Majalisar Tarayya na Gwale Garba Diso
Ɗan Majalisar Tarayya na Gwale Garba Diso

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA MAI GIRMA ƊAN MAJALISAR TARAYYA, MAZABAR GWALE

Zuwa Ga:
Mai Girma [Hon. Garba Ibrahim Diso],
Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya,
Mazabar Gwale,

Mu, jama’ar Gwale, muna rubuto maka wannan wasiƙa ne domin mu bayyana ɓacin rai da takaicinmu game da yadda kake wakiltar mu a majalisar tarayya. An zaɓe ka ne domin ka kare muradunmu, ka saurari matsalolinmu, kuma ka yi aiki tuƙuru domin ci gaban al’ummarmu. Amma abin takaici, ayyukanka (ko rashin aikinka) sun kasa kai matsayin da muke tsammani.

Mun tuna lokacin zaɓe da ya gabata, lokacin da ka zo wurinmu da hannaye a buɗe kana roƙonmu mu zaɓe ka. Ka yi mana alƙawari cewa za ka zama muryarmu, za ka saurari koke-kokenmu, kuma za ka yi aiki domin ci gabanmu. Mun gaskata ka, muka baka amana.

Amma me ka yi tun daga lokacin zuwa yanzu? Fiye da watanni biyar kenan mutanen Hausawa Gwale da ke ƙarƙashin Filin D.O. na’urar bada hasken wutar lantarki (Transformer) suna cikin duhu saboda rashin wutar lantarki. Duk da yawan roƙon da aka yi, har yanzu ba a gyara injin wutar da ya lalace ba. Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici!

Shirunka da shiru da rashin kulawa sun zama shaida ta rashin kasancewarka tare da jama’arka. Ka kasa zuwa ka saurari matsalolinmu, ko ka kawo mafita. Jama’arka suna cikin wahala, amma kai kana zaune ka nuna ko unkula wata ba ka da wata damuwa.

Daraktoci 6 Na Ma’aikatar Tsaro Ta Kasa Sun Faɗa Komar Yan Bindiga

Mun kuma tuna lokacin da muka gana da kai kafin zaɓen 2023, lokacin da ka nuna sha’awar sake tsayawa. Mun faɗa maka matsalolinmu kai tsaye, ka kuma yi alƙawarin gyara abubuwa. Ka ce za ka yi aiki dominmu, kuma za ka kawo canji. Ka roƙi mu sake zaɓenka, muka yi hakan. Amma me ya canza? Babu komai.

Mun sani akwai kuɗaɗe da ake warewa ga ofishinka domin ayyukan mazaba. Mun san yawan kuɗin da aka tanada domin cigaban yankinmu. Mun kuma san cewa akwai tallafi da albarkatu da kake da kake samu a matsayinka na wakilin Gwale kuma shugaban kwamitin majalisa. Ba jahilai ba ne mu, muna karantawa ko sauraren labarai, muna bibiyar yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗenta.

Saboda haka, ba za mu ƙara roƙonka da ka gyara tsohowar ‘transformer’ ɗin ba, muna nema, ba roƙo ba, da ka kawo mana sabuwa a unguwarmu. Mun san kana da ikon yin hakan. Lokacin uzuri ya wuce.

A halin yanzu, wasu wakilai kamar na Kano Municipal da Bichi suna aiki tukuru a mazabunsu. Suna gyara hanyoyi, suna kawo abubuwan more rayuwa, suna tallafa wa ɗalibai da cikakken gurbin karatu har ma da kuɗin alawus na wata-wata, wasu ma suna tura su ƙasashen waje karatu, suna kuma sama musu ayyuka masu albashi mai tsoka. Haka kuma suna magana a gaban majalisa suna kare buƙatun mutanensu. To, me ya hana ka zama irinsu?

Muna roƙonka ka tsaya ka yi nazari: Shin da gaske kana wakiltar jama’ar Gwale ne? Idan amsar ba haka ce, to muna buƙatar ka yi murabus. Rashin aikinka yana nuna gazawa da cin amanar amincewar da muka ba ka.

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

Mu a bayyane muke faɗi: idan ba za ka iya yin aikin da aka ba ka ba, lokaci ya yi da za ka sauka daga mulki. Jama’ar Gwale ba za su ƙara yarda a raina su ba. Kuma idan ba ka yi murabus da kanka ba, muna shirye mu ƙaddamar da ƙuri’ar rashin amincewa da kai, mu kuma fara aikin kiran ka gida, domin a maye gurbin ka da wanda zai iya yin aiki yadda ya dace.

Muna jiran martaninka da aikinka.

Da girmamawa,
Hamisu Isyaku Ibrahim Hausawa
Mazabar Gwale,
Jihar Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...