Ɗalubai Sun Hallaka Malaminsu A Sanadiyar Chacha
Daga Wakilinmu
Wani Malami ya haɗu da ajalinsa sakamakon dukan Kawo wuka da ɗaliban sa sukai masa a Ogbomosho a jihar Oyo.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Malamin Makarantar Mista Fatai Adegoke, na makarantar Soun High School, ya rasu cikin rashin sa’a bayan da ɗalibansa suka kai masa mummunan hari yayin da yake ƙoƙarin hana su caca a lokacin karatu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mista Adegoke ya tsawatar wa wata ƙungiyar ɗalibai da aka kama suna yin caca a cikin aji. A fusace, ɗaliban suka yi masa kwanton bauna inda suka ji masa rauni mai tsanani gaske, har ma da karya ƙafafunsa biyu. An garzaya da shi asibiti, amma daga baya ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Ziyarartar Makarantun Kwana
“Da zafi a zuciya da takaici, muna alhinin wannan mutuwa ta ban tausayi da za a iya ta Mista Fatai Adegoke, malami mai kwazo da sadaukar da kai wanda ɗalibansa suka kai masa hari yayin da yake ƙoƙarin hana su yin caca a lokacin makaranta,” in ji wata sanarwa daga ƙungiyar malamai a sakon su na ta’aziya.
“Wannan mummunan aiki ba kawai hari ne ga mutum ɗaya ba, har ila yau cin fuska ne ga dukan sana’ar koyarwa da ilimi baki ɗaya.”
Sanarwar ta kuma yi kira Ƙungiyar Malamai ta Najeriya (NUT), hukumar TESCOM, da jami’an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa kan waɗanda suka aikata laifin, tare da jaddada bukatar iyaye yaran su ɗauki alhakin halayen ’ya’yansu.
Malamai sun bayyana lamarin a matsayin alamari mai muni da tabarbarewar tarbiyya a makarantu da kuma gidaje don haka suna roƙon hukumomi da masu ruwa da tsaki a fanin ilimi su kara sanye idanun da kuma dawo da tsaro da ladabi a cikin cibiyoyin ilimi.
Read also: Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun 8 masu zaman kansu
Shugaba Donald Trump Ya Soke Visa Dubu 80 Ta ‘Yan Najeriya Da Wasu Kasashen Waje
Majiyarmu ta yi ƙoƙarin tuntuɓar mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, domin tabbatar da labarin, amma bai amsa waya ba. A halin yanzu, rahotanni sun ce ɗaliban da suka aikata laifin sun gudu, abin da ke ƙara haifar da fushin jama’a wanda hakan yake ƙara sanya zaman dar-dar a cikin al’umma.



























