Ana Cikiyar Rahama Abdulganiyu Mai Shekara 16
Daga Sunusi K/Na’isa
Mun samu sanarwar bata yarinya budurwa mai suna Rahama Abdulganiyu Tijjani.
Rahama Abdulganiyu Tijjani mai matsakaicin tsaho, shekarunta goma sha shida (16), baka,ta bata tana sanye da atamfa da mayafi mai kalar ruwan gold.
Rahama ta baro Sabuwar Gandu zuwa Fandanka da misalin karfe 6:30 na Yamma ranar Lahadi 26/10/2025, amma har zuwa yanzu ba a ganta ba kuma babu labarin inda take.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Read also: Kwararriyar Mai Karanta Labarai Lami Maccido Ta Rasu Tana da Shekara 72
Read also: Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet
Ga Wani Labarin:“Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya
Don Allah idan an ga Rahama Abdulganiyu a kaita gidan Abdullahi Idris Kofarnaisa a unguwar Yankusa daura da gidan B A Bello ko gidan Mai unguwar Yankusa ko ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma a kira waɗannan nambobi: 08030738322, 0701 467 0961
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya bayyanata cikin aminci.



























