….Yan Jaridu sun yi tsokaci..
Daga Adita
Ka taimaka da Isar da Sako:
Read also: Mutuwar Aminu Dantata Babban Rashi ne Ga Ƙasa Da Ma Duniya Baki Ɗaya- Gerawa
Rahoton wata Cibiyar Raya Dimokuraɗiyya da Taimakawa Harkokin Zaɓe a Duniya (IDEA), ya bayyana cewa ‘yancin gudanar da aikin jarida ya samu koma baya mafi muni cikin shekaru biyar da suka gabata, wanda ba’a taɓa gani ba a cikin shekaru 50.
Rahoton cibiyar ya bayyana ƙasashen Afghanistan da Burkina Faso da kuma Myanmar a matsayin waɗanda ke sahun gaba-gaba a ƙasashen da aka samu na koma bayan ‘yancin gudanar da aikin jaridar a faɗin duniya. Haka kuma ƙasar Koriya ta Kudu na matsayin ta huɗu dake biye da su, in ji rahoton.
Rahoton ya ce yawancin matsalar nada nasaba da yadda gwamnatoci da ‘yan siyasa ke yawan zargin ‘yan jarida da bata musu suna da kuma yaɗa labaran ƙarya akansu.
Rahotan ya kuma ce sama da kashi 54 na ƙasashe a faɗin duniya na fuskantar koma baya a ‘yancin gudanar da aikin jaridar, duk da kasancewarsa guda daga cikin manyan alamomi biyar na wanzuwar dimokuraɗiyya a kowace ƙasa.
Jaridar STENTOR- Hausa ta yi duba kan wannan rahoton tare da hira da wasu yan jaridu a Kano-Najeriya dangane da yadda wanna cibiya ta gudanar binciken har ta kai ga samun wanna rahoton.
Abubakar Abdulkadir Dangambo, gogage ne a fanin samo labari da kuma yaɗa shi a kafofin yaɗa labarai, ya ce rahoton kusan haka yake, amma da akwai kuskunda, wato ya kamata wanna cibiya tai duba ga wasu ƙasashe, musamman manyan a duniya.
Ya ce ya kamata da cibiyar ta Faɗaɗa binciken ta har zuwa manya ƙasashen da suka cigaba, ba kawai rahoton ya tsaya akan Afrika ko ƙasashe masu tasowa ba, domin rahoton ya ambaci duniya baki ɗaya ne.
Dangambo wanda shine mamalakin jaridar Independentpost.ng.com kuma Shugaban ƙungiyar yan jaridu ta Intanet a jihar Kano, ya ce cibiyar ya kamata tai dubi a halin da Yan jaridu da kuma aikin jarida ke ciki a manyan kasashe kamar su Amurika da Isra’ila da Gaza, inda aikin da masu gudanar da aikin ke cikin tashin hankali da cin zarafi da ma rasa rayuka a lokacin da suke gudanar da aikin nasu.
” Shin irin wannan rahoton baya kallon irin barnar da ake wa yan jaridu a waɗannan ƙasashe, ballantana ya fito da shi a rahoton sa”.
Aditan, ya ce gaskiya ne aikin jarida na fuskantar tasgaro a nahiyar Afirka, sakamakon rashin fahimtar da wasu shugabannin siyasa ke wa aikin, ” Toh! ita kanta Dimokuraɗiyyar ita ma ai bata tsira ba, domin ba zaka raba jarida da dimokuraɗiyya ba”. In ji shi.
Ya bada misali da ƙasar Najeriya, inda wasu yan jaridun ta kai sun yi ƙaura ko kuma suna gidan gyaran hali sakamakon faɗin gaskiya da fayyace badaƙala ko tona asirin aikata rashin gaskiya da wasu shugabannin suka yi a yayin gudanar da mulkin su, musamman wanda ya shafi bincike kan badaƙalar almundahala. “Amma hakan baya nuna duk irin waɗannan basa faruwa a manyan ƙasashen ba, toh, me yasa cibiyar bata kalli irin kasashen ba? In ji shi.
Read also: Fitaccen ɗan jarida Aliyu Abubakar Getso ya rasu
Dangambo, ya kuma ce shigowar sabuwar manhajar internet ta AI ya kara sukurkutar da aikin musamman ga waɗanda basu san yadda za su yi aiki da shi ba, inda ya ce wasu kan ɗauki bayanai batare da tacewa ba daga na’urar ba sannan su yaɗa kai tsaye, wanda hakan ba ya daga cikin ƙwarewar aikin.
Da ya ke nasa tsokacin, mamalakin jaridar THE TENTACALES.COM, Malam Uba Abdullahi, ya kallubalanci rahoton inda ya ce cibiyar tana sane ta rufi idanunta akan manyan ƙasashen duniya da suke take hakkin ɗan jarida da ma aikin baki ɗaya.
Ya bada misali da ƙasar Amurka da Isra’ila ” Shin wanna cibiya bata san meke faruwa a ƙasar Palastinu a Gaza ba, inda ake kashe yan jaridu a kullum tare da raunana da dama daga cikin su, wanda sanadin hakan suna kwace a asibitoci, ko kuma a hana su gudanar da aikin nasu baki ɗaya?”
Aditan, ya kallubalanci cibiyar cewar idan da gangan ta ɗauke idon ta ga duban waɗannan kasashe da makamantansu, toh, ta koma ta sake haɗa rahoton, idan kuma bisa mantuwa ne ya kamata cibiyar ta tuna.
Ya ce bashi da ko ja aikin jarida yana samun kalubale da koma baya, amma ba kawai a Kasashen Afrika ba ko kuma ƙasashe masu tasowa ba, har da manyan ƙasashe da ake kira (Super powers).
Makamancin Labarin: Ƙungiyar likitoci ta janye yajin aikin gargaɗin da ta fara
Shugaban cibiyar Casas-Zamor ya bayyana damuwa kan halin da dimokuraɗiyya a duniya ke ciki a yanzu, a yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP,
‘Yancin gudanar da aikin jaridar ya samu koma baya ne a ƙasashe 43 a faɗin dukkan nahiyoyi, ciki har da 15 daga Afrika da kuma wasu 15 a Turai.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
An tattara bayanan ne a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2024, a don haka bai ƙunshi irin matakan da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka ba bayan dawowarsa mulki, waɗanda suka taka rawa matuƙa wajen haifar da koma bayan aikin jarida a ƙasar.
Cibiyar ta haƙiƙance cewa, irin rahotannin da ta tattara a lokutan zaɓe a ƙarshen shekarar 2024 da kuma watannin farko na 2025 abun damuwa ne matuƙa, kasancewar matakan da Amurka ta ɗauka a fannin ka iya shafar duniya baki ɗaya, kuma ba zai haifar da ɗa-mai-ido ga dimokuraɗiyya ba.




























