Litinin Ita Ce 1 Ga Watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira, In ji Sarkin Musulmi
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse
Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar III, ya sanar da Litinin a matsayin ranar farko ta watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Junaidu, wanda kuma shi ne shugaban majalisar shawarwari ta fadar Sarkin Musulmi, a daren Asabar.
A cewar Farfesa Junaidu, hukumar duban wata ta kasa ta tabbatar da cewa ba a samu ganin jaririn watan Rabi’ul Awwal ba a daren Asabar a ko’ina cikin Najeriya, lamarin da ya sanya aka ƙayyade Litinin a matsayin farkon watan.
Haka zalika ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da gudanar da ibada da yin addu’o’in alheri ga ƙasa da al’ummar musulmin a wannan wata mai albarka.




























