Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano
Labarin rasuwar sa ya fito daga ɗannsa kuma ɗan jarida, Auwalu Ali Sufi Utai, da ya sanar wa da kafar yaɗa labarai tabbatar ta (NIGERIAN TRACKER).
A cewar Auwalu, mahaifinsa ya rasu ne bayan fama da jinya, inda ya kasance ɗaya daga cikin ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen aiki tukuru a gidan Rediyon Kano — ɗaya daga cikin tsoffin ƙafar yaɗa labarai mafi dalewa a Najeriya.
Read also: Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus
Marigayin ya rasu ne kwanaki shida da suka gabata, inda ya bar ’ya’ya da jikoki da tattaba-gida da dama.
Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
An haifi Malam Ali Sufi Utai a garin Utai da ke ƙaramar hukumar Wudil, a jihar Kano, kusan shekaru 100 da suka gabata, ya shahara da rikon gaskiya da sadaukarwa a aikinsa na rediyo.
Iftila’i: Yara Biyu Sun Mutu Sakamakon Mamakon Ruwan Sama
Ana sa ran za a gudanar da addu’o’i na musamman domin roƙon rahamar Allah a gare shi, tare da jaje ga iyalansa da al’ummar Wudil gaba ɗaya.




























