Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Mutane 5 sun mutu da yawa sun jikanta sakamakon fashewar bom a Kano

Fashewar bam a bypass
Fashewar bam a bypass

Mutane 5 sun mutu da yawa sun jikanta sakamakon fashewar bom a Kano

Daga Sunusi K/Nai’sa

Aƙalla mutum biyar ne ake zargin sun rasu, yayin da wasu 15 suka samu muggan raunuka sakamakon fashewar wani abu da ake zargin bam ne a Jihar Kano.

Daily trust ta gano yadda fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke yin jigilar ne wanda me yiwa akai sakaci ya fashe.

Lamarin dai ya faru ne a kan titin bypass dake jihar Kano.

“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin kamar bama-baman sojoji ne suka fashe”.

Da ɗumi-ɗumi: Minista Wike ya ce masu ido da kwalli sune matsalar Abuja

“Mutane 15 sun jikkata, kuma abin takaici, guda biyar sun rasu,” in ji Kwamishina.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci da ke kusa da yankin da abin ya faru domin samun kulawar gaggawa.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da kayan fashewar, wadda ta ke kan hanyar zuwa Jihar Yobe.

Har yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da ko motar sojoji ce ke ɗauke da kayan fashewar ba.

Rundunar ‘yan sanda ta bada tabbacin cigaba da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma abin da ya haddasa fashewar abun.

“Za mu samu cikakken bayani bayan kammala bincike,” in ji Kwamishinan.

Hanyar Dan Madanho ta gagari Kundila, mazauna yankin na roƙon Gwmna Abba ya kawo ɗauki

Ya kuma roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da cigaba da harkokinsu na yau da kullum gami da basu tabbacin cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...