Iran Ta Saki Makamai masu Linzamin 150 a Safiyar yau Asabar Akan Ƙasar Israel
Daga Adita
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
A ƙoƙarin ramuwar gayya sakamakon kutse da hare-haren da ƙasar Israel ta kai mata na wanda yai sanadiyar kashe wasu jigajigan Kwamandojinta , Iran ta sake Ƙaddamar da sabon hari da makamai masu Linzami 150 a wani farmaki wanda tai wa laƙabi da sunan “Honest Promise 3”.
A safiyar yau Asabar, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ƙaddamar da sabon harin da makamai masu linzami a kan Isra’ila, wanda ta sanya wa suna “Honest Promise 3”.
Wannan harin ya biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a baya wanda ya yi sanadin mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran da fararen hula da yawa a wasu sassan yankin Gabas ta Tsakiya.
A Iya Karanta Wanna:Iftula’i: Barayin Waya Sun Kashe Wani Haziƙin Ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano
Read also: Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62
Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na Cikin gida Iran, kamar Almayadeen Al-arabiya sun bayyana cewa harin ya ƙunshi jefa manyan makamai masu linzami da kuma wasu jiragen yaƙi marasa matuƙa (drones) zuwa yankunan Isra’ila, da nufin ɗaukar fansa kan abin da Iran ta kira “kisan kai ba tare da wani dalili ba da Isra’ilan ta aikata a kanta.”
Tuni Ma’aikatar tsaron ƙasar Iran ta ce wannan harin wani bangare ne na jerin martanin diflomasiyya na soji da ƙasar ke ɗauka don kare martabarta da tsaron iyakokinta da kuma al’ummarta. Wannan shi ne karo na uku cikin jerin hare-haren da Iran ke daukar nauyin su, wadanda aka sanya wa suna “Honest Promise”, domin mayar da martani ga ƙasar ta Israel tare da nuna mata cewar Iran ta shirya domin gwabza yaƙin.
Iran ta ce hare-haren da Israel ta kamata ya shafi sojojinta da farar hula da kuma abokan ƙawance ta wanda ta lashi takobin ɗaukar fansa.
A Iya Karanta Wanna:Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Yaƙin da mahalkanta ke hangen idan shugabannin duniya ba suyi da gaske ba, to tabbas ka iya zama yaƙin duniya na uku kuma idan ya zamanto hakan Allah ne yasan yawan asarar da za ayi wanda ya shafi rai da ɗinbin dukiya, wanda hakan ka iya kawo rushewar wasu ƙasashe musamman ta fuskar tattalin arziki.




























