Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Iftula’i: Barayin Waya Sun Kashe Wani Haziƙin Ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano

Ma'aikacin jami'ar Northwest Buhai Imam
Ma'aikacin jami'ar Northwest Buhai Imam

Iftula’i: Barayin Waya Sun Kashe Wani Haziƙin Ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano

Daga Abubakar Ibrahim

Daukacin al’ummar Jami’ar Northwest University Kano, na cikin alhinin rashin ɗaya daga cikin ma’aikacin ta, Buhari Imam, wanda ya gamu da ajalinsa a wani hari da barayin waya suka kai masa har gida a unguwar Sheka dake birnin Kano a daren ranar Laraba 11 ga watan Yuni 2025.

Lamarin ya faru ne a wannan rana, da misalin karfe 3:30 na safe a Sheka Sabuwar Abuja, ƙaramar hukumar Kumbotso, jihar Kano. Buhari Imam ya kasance ma’aikaci mai ƙwazo a sashin kuda da gyare-gyare, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gudanar da taro na 7 na cibiyar, wanda aka gudanar da shi a harabar cibiyar a kwanana.

Marigayi Buhari, kafin rasuwar sa dalibi ne a shekarar ƙarshe da yake karatun babbar diploma (HND) a Kano State Polytechnic inda ya karanta (Electrical Engineering), ya shahara da jajircewa da sadaukarwa wajen gudanar da karatunsa da kuma ayyukansa a jami’ar. Mutuwar sa ta jijjiga ma’aikatan jami’ar gami da sanya damuwa a zukatan ma’aikatan jami’ar da kuma sauran al’umma baki ɗaya.
A Iya Karanta Wanna:Nijeria Kasarmu Ta Gado Mai Wuyar Zama 
Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma tsantsar rashin imani, ya jajantawa ‘yan uwa da abokanan aiki na marigayin. Ya kuma yi addu’ar Allah ya kara musu haƙurin da jure rashin, ya kuma yi roƙi Allah ya kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yi a wannan jiha dama ƙasa gaba ɗaya.

Farfesa Kurawa ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro da su binciko waɗanda suka aikata wannan aiki na dabbanci tare da gurfanar da su a gaban Shari’a, haka kuma ya roƙi gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen magance matsalar sace-sacen waya da ta’addanci a yankin Sheka da kuma fadin jihar Kano baki ɗaya.

“Wannan wani bala’i ne mai muni,” in ji Mataimakin Shugaban Jami’ar. “Ba za mu iya ci gaba da rasa matasa masu kwazo ta waɗannan tashe-tashen hankula da ke faruwa ba,” muna ƙara roƙon gwamnati da ta samar da mafita mai ɗorewa kan wannan matsalar kafin abin ya gagari kundila.”
A Iya Karanta Wanna:Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko
Ya ce hukumar Gudanarwar Jami’ar ta sake jaddada ƙudurinta na kare lafiya da jin dadin ma’aikatanta da dalibanta.

Haka kuma shugaban ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su tashi tsaye don magance sha da fatauci miyagun ƙwayoyi domi su ne ummul-abaisu na haddasa irin waɗannan miyagun laifuka a cikin biranen Kano. Zamu ci gaba da tunawa da Buhari Imam, da irin kyawawan dabi’un sa da ƙoƙarin da sadaukarwa da kuma tawali’u.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...