Majalisar Matasan Arewa ta nuna damuwa da matsanancin rashin wutar lantarki a Kano
Daga Wakilinmu
Read also: Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Majalisar matasan arewacin Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana matukar damuwarta dangane da tabarbarewar wutar lantarki a jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Sulaiman Idris ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai, NYA ta ce, ci gaba da katsewar wutar lantarki da mazauna yankin da ‘yan kasuwa ke fuskanta ya jawo wahalhalu, da tafiyar hawainiya da harkokin tattalin arziki, tare da rage jin dadin rayuwa a fadin jihar.
“Wannan mawuyacin hali ya nuna yadda Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) ya gaza wajen raba wutar lantarki yadda ya kamata a cikin jihar. Hakan kuma ya nuna rashin cika alkawuran da Gwamnatin Tarayya ta yi na tabbatar da samar da wutar lantarki mai inganci ga ‘yan Najeriya.
Makamancin Labarin:Al’ummar Unguwar Lokon Makera A Kano Sun Koka da Kamfar Wutar Lantarki
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Kungiyar ta Matasan ta ce, duk da tabbacin da aka yi ta bayar wa, amma har yanzu an kasa magance matsalar.
“Saboda haka, muna amfani da wannan kafar don yin kira ga masu ruwa da tsaki – ciki har da shugabannin al’umma, masana makamashi, da masu tsara manufofi – da su gaggauta yin taro tare da yin shawarwari kan hanyoyin magance matsalar wutar lantarki ta Kano.”
“Wannan batu na bukatar kulawa cikin gaggawa da kuma kokarin hadin gwiwa a dukkan matakai”.
“Bugu da ƙari, muna yin kira mai ƙarfi ga masu hannu da shuni, masu zuba jari, da masu masana’antu a Kano da yankin Arewa, da kuma duk faɗin Najeriya: Yanzu ne lokacin da za a saka hannun jari a kamfanonin samar da wutar lantarki da rarrabawa masu zaman kansu. Kano na buƙatar sabbin hanyoyin samar da wutar lantarki na gida don biyan buƙatunta na wutar lantarki”.
Read also: Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Makamancin Labarin:Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar Sama Da Naira Miliyan 375
Kungiyar matasan ta ce, ta yi imanin cewa, tare da hadin kai da kirkire-kirkire, da saka hannun jari, Kano za ta iya shawo kan kalubalen wutar lantarkin da take fama da shi, ta kuma zama abin koyi ga sauran yankuna a Najeriya.




























