BUDADDIYAR WASIKA
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: Alamun Murar Tsuntsaye ta Bulla A Kano, Gwamnati ta Ce Babu Fargaba
Assalam alaikum warahmatullahi Ta’ala Wabara Katahu.
Bayan Gaisuwa irin ta Addinin Musulunci ina yi mana fatan Alheri da kuma fatan dacewa a ko da yaushe gami da rokon Allah (SWA) ya kara kare jihar mu mai albarka da ƙaruwar arziki.
A Kullum fatanmu Al’ummar Kofar -Naisa ta samu ci gaba ta kowane fanni kama daga ilmi, lafiya, sana’a da duk wani bangaren ci gaban rayuwa – Sai dai Kash! a yanzu dai abubuwa baya suke komawa, ban sani ba rashin kulawa ne gami da rashin mai da hankali daga jagorori ne, ko kuma daga dattawan Unguwar? Abubuwa da dama da kuma fannoni masu yawa da dama sai ƙara sukurkuccewa su ke a halin yanzu.
A Iya Karanta Wanna:ASIBITIN KWARARRU NA BAUCHI DA KE BACAS, NA FISKANTAR KALUBALE NA ADANA GAWA
Dalilin wannan rubutun shine ganin yadda aka maida Asibitin sha-ka-tafi, wato Kofar Naisa Primary Healthcare (PHC) ya zama wani yasashen wuri da baya amfanar da al’umma ta kowane fuska wanda a yanzu ya ɗako hanyar lalacewa gaba ɗaya ma, tun bayan dena aiki da wurin, a inda mahukuntan Ƙaramar hukumar mu ta Gwale suka janye Wakilinsu, wato ma’aikatan Asibitin. Wanda a halin yanzu mun samu labarin Asibitin ya zama sansanin Yan GARUWA da YAN SHAYE-SHAYE da YAN SHARE waje zauna.
Read also: Kano na Alhini Rashin Mahaifiyar ‘Yan Biyar, Ta Rasu Bayan Haihuwa
Wanda lashakka hakan ci baya ne, musamman a harkar lafiya a wannan unguwa da kuma makobtanta, amma ba wanda ya kula tare da yin la-ubali da Asibitin, idan kuma har ana wani motsi ne domin ceto asibitin toh, har yanzu abun bai bayyana garemu bah, balantana mu yi sam barka.
Duk da cewa wanna unguwa ta Kofarnaisa tana da gata kasancewar tana ɗauke da manyan mutane, waɗanda suka haɗar da ‘yan siyasa da attajirai manyan Malamai kai bilhasali ma Kwamishina lafiya na jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf haifafan ɗan unguwane, amma tuwanmu ya yi ruwa.
A saboda haka muke miko budaddiyar wasika ga Mai girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda kuma shima dan Ƙaramar hukumar Gwale ne, da ya kalli halin da jama’ar wanna unguwa suke ciki domin a fidda jaki daga duma.
Ko musu babu, munsani wanna gwamnati ta Abba Gida-Gida ta bawa ilimi da lafiya kulawar gaske, amma mu unguwar mu ta zama koma baya, musamman a fannin da sha fi lafiya, wace akewa lakabi da babu mai fishi da ke.
Kai ko da wurin bazai koma asibiti ba kamar yadda muka taso muka gani bah, yakamata mahukunta suyi duba da wasu abubuwa masu amfani kamar gurin horas da sana’o’i (Skills accusation center) ko Islamiyya da makamantan su domin amfanin matasan wanna unguwa. Amma a hankali wurin yazama kamar ma ba wurin al’ummar kofar Naisa ba.
Read also: Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano
A Iya Karanta Wanna:NNPCL: Zai koma aikin haƙar ɗanyen Mai a Arewacin Najeriya
Ina amfani da wanna kafa domin rokon mahukunta da shugabanni da duk masu faɗa-a-ji suyi duba na tsanaki kan wannan wuri domin farfaɗo da shi don ya ci gaba da amfanar da al’ummar wannan yanki namu na kofar Naisa da ma makobtanta.



























