YAN BANGA DA MUTANE 19 SUN RASU A YAYIN ARANGAMA DA YAN BINDIGA A YANKIN DA GWAMNAN BAUCHI YA FITO
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Bauchi: Ƙungiyar Fulani Sullubawa Sun Yi Alwashin Samar Da Haɗin Kai Don Ingantaccen Tsaro
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kai mummunan harin Yan bindiga kan wasu Yan banga da mutanen kauyukan karamar hukumar Alkaleri Yankin da Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya fito.
Harin da ake kyautata zaton ‘yan bindigar sun kai a wasu ƙauyukan gwana ya kai ga kashe mutanen gari da Yan sintiri a ƙalla 19 nan take, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ƙauyukan da aka kai harin na gundumar Gwana ne da ke ƙaramar hukumar Alkaleri kamar yadda rahotanni daga yankin suka bayyana cewa ƙauyukan da aka kai harin sun hada da Mansur, Digare da Sabuwar Sara da kuma Yalo, Kuma an kai harin ne da yammacin ranar Asabar.
Read also: Rikicin Manoma da Makiyaya Yai Sanadiyar Rasa Rayukan Ƴansanda 5 da Ɗanagaji A Bauchi
A Iya Karanta Wanna:MA’AIKATA 4 NA MATATAR RUWAN GUBI DAM, BAUCHI SUN RASU A BAKIN AIKI
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bauchi Sani-Omolori Aliyu ya ziyarci inda ta’asar ta abku domin gudanar da bincike a kan lamarin, kuma ya tura ƙwararrun jami’ai don ci gaba da bin sawu da binciken ‘Yan-ina-da-kisan.
A lokacin da ya ke Alkaleri, kwamishinan ‘yan sandan ya tattauna da masu ruwa da tsaki, sannan ya bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa, ya kuma baiwa ‘yan sanda goyon baya domin ci gaba da samar da tsaro kamar yadda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, musamnan ganin lamarin ya ɗauki sabon salon salwantar da rayukan bayin Allah.
A cewer Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar a wannan Litinin, ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan ya yi Allah wadai da kashe-kashen, tare da nuna alhininsa kan hasarar rayuka da aka yi sakamakon wannan mummunan hari.
Read also: AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI
A Iya Karanta Wanna:Mutane 148 sun mutu a wani haɗarin kwale-kwale da ya faru a Congo
Rundunar ta umurci wata tawaga ta musamman da ta ƙara zage damtse wajen ganin an kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki da kuma mutanen da su ke da alaka da duk wani ta’addanci da ake yi a Yankin na Alkaleri da sauran sassan jihar Bauchi.



























