Nasir El-Rufa’i Ya ce Bashi da Damar Yin Kutse Ga Wayar NSA Ribado, Amma Salon Adawar Siyasa Ce
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta zargin kutse da sauraron tattaunawar wayar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ko umartar wani da ya aikata hakan.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a yau Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, yayin da yake bayar da shaida a shari’ar da ake yi masa a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Read also: Kotun Kano Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa Sau Bakwai Kowanne Saboda Kashe Mace Da Yara Shida
Yayin da lauyansa, Paul Erokoro, SAN, ke yi masa tambayoyi, tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewa bai taɓa mallakar na’urar da ake amfani da ita wajen kutse ko sauraron tattaunawar waya ba, kuma ba shi da ƙwarewar fasaha ta yin hakan.
Ya kuma musanta cewa yana da damar shiga hanyoyin sadarwa ko na’urorin NSA Nuhu Ribadu.
Da yake bayanin kalaman da ya yi a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, El-Rufai ya ce furucinsa na cewa suna sauraron kiran wayoyin jami’an gwamnati salon magana ne na siyasa, ba wai yana amsa laifin kutse ba.
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Ya ce lokacin da ya yi amfani da kalmar “mu”, yana nufin ’yan siyasar adawa ne, kuma ya yi amfani da kalmar “an saurari wayoyinsu” ne domin ƙara fito da yadda ’yan adawa ke jin zafin matakan gwamnati.
A cewarsa, kalaman nasa sun kasance ƙarin gishiri da salon mayar da martani na siyasa, ba furucin cewa shi da kansa ya kutsa wayar Ribadu ba domin nadalar Bayanin ba.
Ana tuhumar tsohon gwamnan ne a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin kutse da sauraron tattaunawar wayar NSA ba bisa ƙa’ida ba, samun bayanan sirri ba tare da izini ba, da wasu laifuffukan da suka shafi tsaron ƙasa da hanyoyin sadarwa.
A ranar 26 ga Oktoba, 2026, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da buƙatar El-Rufai ta neman a sallame shi ba tare da ya kare kansa ba, inda ta ce hujjojin da masu gabatar da ƙara suka gabatar sun isa a bukaci ya amsa zarge-zargen.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Sai dai matakin kotun ba yana nufin an tabbatar da cewa El-Rufai ya aikata laifin ba ne. Har yanzu shari’ar tana gudana, kuma kotu ba ta yanke hukunci kan ko yana da laifi ko babu ba.
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta dage ci gaba da suraron shari’ar zuwa bayan zaɓen shekara mai kamawa ta 15 da 16 ga watan Fabrairu 2027.



























