Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers
Daga Adita
Read also: Hukumar Zabe Ta Jihar Kano Ta Rage Kudin Siyan Fom Na Shiga Zaben Ƙanana Hukumomi
Shugaban kasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikicin siyasa da jihar ta samu kanta tsawon lokaci.
Tinubu ya ayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a kan matsalar siyasar da ke addabar jihar ta Rivers, a inda manyan ‘yan siyasar jihar ke gwajin kwanji tsawon lokaci, musamman tsakanin Gwamna da kuma majalisar dokoki ta jihar.
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna a tsawon lokaci.
A Karanta Wanna:Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya
Read also: BASHI NA DAF DA DURKUSAR DA NAJERIYA
” Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi mu yi duba tare da aiki da sashi na 305 na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025
An dakatar da gwamnan Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa na tsawon wata shida.
Tinubu yace yayi iyakar bakin kokarinsa kan yadda za a magance matsalar to amma duka bangarorin sun yi la-ubali gami da watsi da yunkurin nasa.
A Karanta Wanna:Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Haka nan shugaban ƙasa ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu kokarin amma hakar ta ci tura.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
A Karanta Wanna:Ramadan: Gwamnan Kano ya baiwa kungiyoyin ‘Yan jaridu tallafin shinkafa buhu 450
A yanzu haka ta tabbata babu wata sahihiyar zababiyar gwamnati a jihar Rivers.



























