Hukumar Zabe Ta Jihar Kano Ta Rage Kudin Siyan Fom Na Shiga Zaben….
Daga Ado Abdu K/Naisa
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Shugaban hukumar zabe Mai zaman kanta ta jihar Kano, farfesa Sani lawan malunfashi ya bayyana sabon farashin kudin fom na waɗanda za su tsaya takarar shugabancin kanana hukumomi da Kansiloli a jihar Kano.
Malumfashi ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a shelkwatar hukumar a yau Juma’a.
A Karanta Wanna:Farafesa Ibrahim Maibushira Ya Zama Shugaban Kungiyar Safinatul-Khair A Kano
Read also: Kotin ƙoli: Nura Husaini Ya Bayyana Nasarar Gwamna Abba A Matsyin Nasara Ga Al’ummar Kano
Malumfashi ya ce hakika Wasu jam’iyu guda uku sun Kai Kara kotu domin rage kudin fom na ‘yantakara, don haka hukumar ta yi biyayya ga umarnin kotun.
Shugaban hukumar zaben ta jiha, ya ce bayan tattaunawa da sukai sun rage kuɗin fom na tsayawa neman takarar shugabancin karamar hukuma daga naira miliyan 10 zuwa miliyan 9. Haka zalika na tsayawa takarar Kansila an rageshi daga naira miliyan 5 zuwa miliyan 4.
A Karanta Wanna:Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi da Kwacan Waya: Tayi Holin Wasu Matasa Ga ‘Yanjaridu A Kano
Read also: Canja Jam’iyya a Siyasar Kano Ya Zo a Kan Lokaci, Kuma Muniface Mai Kyau– Inuwa Waya
Malumfashi ya Kara da cewar a gobe Asabar 14 ga watan satumba wannan shekarar ta 2024 hukumar zata rufe karbar sunayan ‘yan takara daga jam’iyu daban-daban, tare da sanar da duk mai bukatar siyan fom na takara ya garzaya banki domin siyan nasa.




























