Mun Fasara Littafin Sunayen Ma’aikatu Da Hausa…
Daga Sunusi Kofar Na’isa
Read also: Karamar Hukumar Ghari Ta Raba Takardun Daukar Aiki Ga Malamai 50
Wani fittaccen Dan jarida da ke aiki a gidan radiyon Tarayya ta Pyramid FM (Mai gajeran zango) da ke jihar Kano, Muhammad Adamu Abubakar, ya ce ya rubuta littafi cikin harshen Hausa mai dauke da sunayen hukumomin gwamnatin tarayya da jiha da ma hukumomi masu zaman kansu ne da nufin taimakawa abokan aiki ‘yan jaridu musamman masu aikin fassara a kafofin yaɗa labaru domin samun sauƙin aikin da kuma inganta aikin kamar yadda ya kamata.
Adamu wanda Edita ne a gidan radiyon tarayya Pyramid ya ce haka kuma yana daga cikin muhimmancin samar da littafin domin tallafawa al’umma da ɗalibai da ma matasan mu da suka tsinci kansu cikin gurbattacciyar hausa sakamakon sauraren sabbin kafofin sadarwa.Ya ce wallafar littafin sunayen hukumomi zai kuma taimakawa masu bincike a fanin ilimi.
Dan jarida Muhammad, wanda kuma shi ne wakilin gidan radiyo na Pyramid a majalisar dokoki ta jihar Kano, ya ce ” Littafin ya ƙunshi sunayen hukumomin da ma’aikatun gwamnatin da ma masu zaman kansu da kuma fassara sunayen zuwa Hausa don amfani da kuma Saukakawa ‘yan Jarida da masu fassara yayin gudanar da ayyukan su na yau da kullum”. Inji Muhammad.
KA KARANTA WANNA:Addu’ar Magabata ita ce Sirin Samun Zaman Lafiya a Mararabar Gurku, Inji Sarkin Hausawa Mani
“Mun rubuta wannan Littafin ne don amfanar da abokan aikinmu masu tasowa musamman a harkokin fassara daga Turancin Ingilishi zuwa Hausa da ma sauran su,” marubucin ya jaddada.
Daga bisani Marubucin, ya bukaci masu fassara musamman ‘yan Jarida wala-allah na gidan radiyo ko talabijin ko kuma ta dab’e wato (print), har masu wallafa a yanar intanet da sauran su, da su rinƙa amfani da Littafin wanda zai taimaka gayya wajen ci gaban aikinsu baki daya.
KA KARANTA WANNA:DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)
Ya kuma ce nan gaba da akwai yiwuwar faɗaɗa littafin, yadda zai kunshi wasu muhimman sunayen kungiyoyi zarar bukatar hakan ta taso.
Read also: ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Buƙatar Su
KA KARANTA WANNA:Makarantar Zam-Zam International ta Yaye Ɗalibai 28 Mahaddata Al-Qur’ani, Ciki Har da Asiya Usman
Muhammad Adamu ya godewa wadanda suka taimaka wajen wallafar littafin musamman wani wakilin jama’a wato ɗan siyasa da ya bashi gudun mawa don dabbaka abin alheri domin ‘yan baya su amfana.



























