Sojoji Sun Lakume Manyan Kwamandojin Bello Turji Guda 7, Da Sauran Yaransa 24
Rundunar Tsaron Sojojin Nijeriya, Fansan Yamma ta samu nasarar kauwar da ‘yan ta’adda su ashirin da huɗu, a cikinsu akwai manyan kwamandojin hatsabibin Dan ta’addanan da aka fi sani da Bello Turji, a bata kashin da ta ɗauki tsawon sati ana bugawa a arewa maso yamma Nijeriya.
Read also: Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Zagazola Makama, ya bada rahoton cewar sumamen da kwararrun jami’an sojan Nijeriya a karkashin Bataliya ta ɗaya (1) da Kuma sojin Ruwan na kasar masu kula da Jiragen ruwa a maboyarsu, wannan nasarar ta samu ne ranar 22 ga janeru, 2025, a kauyen Gebe, karamar hukumar Isa dake jihar Sokoto.
Duba da samun Rahotonnin sirri, karon battar da aka ɗauki sati ana yi wanda aka tsara don tarwatsa wuraren da Bello Turji ke ayyukansa da maboyarsa haɗa da sansanoninsa da suke a kananan hukumomin Shinkafi da Isa,a Wuraren da suke ta’adanchin nasu. Sumamen ya haɗa da Sojin kasa da Kuma Hari daga sama da tallafin jami’an leken asiri.
Ka Iya Karanta Wanna:Alamun Murar Tsuntsaye ta Bulla A Kano, Gwamnati ta Ce Babu Fargaba
Daga cikin kwamandojin da aka samu nasarar turawa barzahu akwai, Abu Dan Shehu da Jabbi Dogo da Dan Kane da Basiru Yellow da Kabiru Gebe da Bello Buba da Dan Inna Kahon Saniya (wanda aka fi sani da yafi Bahaushe).
Read also: Babban Yaron Ɗan Ta’adda Bello Turji, Yalo Ɗan Bokolo ya Baƙunci Lahira
Waɗannan kwamandojin sune jigon duk wani hari, ko kai ta’adanci, tare da kula da duk wata gudanarwa da safarar makamai a tsakanin sassan kasar nan. Kautar dasu zai zama wani babban nakasu ga shugabancin da kuma gudarwar tawagar ‘yan ta’addan.
Ka Iya Karanta Wanna:Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Bulla A Nijeriya
Kyakkyawan harin mai cike da nasara ya gudana ta hanyar kwanton bauna da gudanar da binciken siri gami da tarwatsa sansanonin ‘yan ta’addar da kuma harin Jiragen sama. Hakan ya sanya an samu Makamai, Harsasai da baburan hawa wanda ‘yan ta’addar ke amfani dasu domin yakar al’ummar da basu ji ba basu gani ba da kuma kwace musu dukiya gami da satar mutane da dabbobin su.
A ‘yan watanninan, rundunar Sojin kasar ta samu nasarar kauda ‘yan ta’adda saboda rahotonnin yawan samun ta’adanci, satar jama’a da kuma kashe jama’a da jami’an tsaro a jihohin Zamfara, Sokoto,katsina da Birnin Kebbi.
Wannan harin kwantan baunar da jamian suka yi akan kwamandojin guda Bakwai hadi da tarwatsa maboyansu tare da tabbatar da kashe ‘Da ga Bello Turji, na tabbatar da yunƙurin da ake na yaƙi da ‘yan ta’adda a Arewa maso yamma gaba daya.
Read also: DA DUMI-DUMI; Jami’an Hukumar DSS Ta Kama Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo
Ka Iya Karanta Wanna:Daukewar Wutar Lantarki ta ‘Yan Dakikoki ta Jawo Biyan Diyar Sama Da Naira Miliyan 375
A labarin da muke samu makusantansa suna ta janye waɗanda suka ji raunuka tare da shi Turjin domin samun mafaka a karamar hukumar Maradun.





























Maikudi Marafa
January 23, 2025 at 11:42 am
Hakan wata nasara ce ga rundunar sojojin Najeriya Wajen yakar Yan ta’addar.
Allah ya bada nasara wa ga sojojin kasar nan