Connect with us

Hi, what are you looking for?

Lafiya

Majalisar Dokokin Jihar Kano Zata Tallafawa Hukumar DMCSA Don Ta Cimma Gaci

Majalisar Kano
Majalisar Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano Zata Tallafawa Hukumar DMCSA Don Ta Cimma Gaci

Daga Sunusi K/Na’isa

A wani ho66asa na mussaman don ha6aka harkar kiwon lafiya, Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tallafawa Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar nan don ganin ta sauke nauyin da aka dora mata.

Mambobin Kwamitin Lafiya na Majalisa ne suka bayyana haka a lokacin da suka kar6i bakuncin shugabannin Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar Kano (DMCSA), ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar na hukumar, Famasist Gali Sule, wadanda suka je harabar majalisar don yiwa ‘yan Kwamitin bayani a kan ayyukan ma’aikatar da kuma tarin nasarori da ta samu a shekara ɗaya da rabi.

Da yake jawabi a lokacin ganawar, Mataimakin Kakakin Majalisar, Honorabil Muhammad Bello Butu-Butu ya tabbatar wa da shugabannin Hukumar ta DMCSA cikakken goyon bayan Majalisar domin inganta samar da magunguna a fadin jihar nan.

Daga nan sai Mataimakin Kakakin Majalisar ya yabawa irin namijin kokari na shugabanni da ma ma’aikatan Hukumar Samar da Magunguna ta Jiha.

Alamun Murar Tsuntsaye ta Bulla A Kano, Gwamnati ta Ce Babu Fargaba

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar Dokoki Ta Jihar nan, Honorabil Zakariyya Alasan Ishaq, wanda kuma shi ne dan majalisa mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Kura da Garun Malam, ya jinjinawa Famasist Gali Sule sakamakon tarin nasarori da ya samu a cikin gajeren lokaci.

A tasa gudunmawar, Dan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungogo a zauren majalisar, Honoabil Aminu Sa’ad Ungogo ya yi kira da sauran hukumomi a jihar nan da su yi koyi da Hukumar Samar da Magunguna ta hanyar zage damtse domin ciyar da jihar nan gaba.

Da yake jawabi tun da fari, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, Famasist Gali Sule ya ce sun je Zauren Majalisar ne don sanar da ‘yan Kwamitin irin aikace-aikacen hukumarsa da nasarori da ta samu da kuma kalubale da take fuskanta.

Famasist Gali Sule ya kara da cewa kadan daga cikin irin nasarorin da hukumar ta samu sun hada da biyan sama da kaso 60 na bashin da ake bin wannan hukuma wanda aka gada daga gwamnatin da ta gabata, da kuma samar da ingantattun magunguna masu rahusa daga kaso 30 zuwa kaso 96.

Ko Kasan Sabbin Kwamishinonin Da Gwamna Kano Abba Yusuf Ya Naɗa?

Haka kuma, yawan asibitocin da Hukumar take bai wa magunguna sun karu daga guda 814 zuwa 890. Haka zalika, Hukumar tana gudanar da taron masu ruwa da tsaki duk bayan watanni uku don tabbatar da ana yin komai bisa tsari kuma a bude, in ji shi, kamar yadda Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar DMCSA Farouk Isa Musa ya aikewa kafar sadarwa ta The STENTORNEWS.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...