Daga Muazu Hardawa, Bauchi
A wani al’amari mai kama da banbarakwai, Alkalai a garin Azare dake jihar Bauchi a Nijeriya sun yi hobbasa na gidauniyar kuɗi don samawa wata matar aure da kuɗi suka karye wa a sanadiyyar cin bashi iskar ‘yanci.
Read also: Fursunoni 61 Sun Haddace Alƙur’ani Mai Tsarki a Gidan Gyaran Hali na Kano
Alkalan sun ce sun yi haka ne saboda lura da su kai da kokarin matar auren na biyan bashin da ake bin ta ta yin aikin wankau domin ta sauke nauyin dake kanta na biyan bashin, har naira dubu ɗari (₦100,000) da ta karba domin yin kasuwanci.
Matar Mai suna Zakiya Lawan ta ci bashin kuɗin mutana ne domin yin kasuwanci amma saboda mijinta ya gudu ya barta da yara bisa halin matsin rayuwa da ake ciki, kuma yaran sun yi fama da rashin lafiya a inda tai musu jinya da ciyar da su da kudin, hakan yasa kuɗin suka salwanta.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Ganin haka ta kama sana’ar wankau na kayan mutane da nufin ko ta samu kudin da zata biya masu binta bashin, amma hakan ya-ci-tura, sai dai ta biya kusan naira dubu arba’in (₦40,000) daga cikin kundin.
Sakamakon rashin biyan ragowar kuɗin, aka kaita kara kotun Shari’a ta ɗaya da ke Nassarawa Azare, nan take aka ingiza keyarta zuwa gidan gyaran hali na garin Azare ɗauke da jaririyar ta.
A Iya Karanta Wanna:Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Bulla A Nijeriya
Ganin wanna hali da matar ta shiga ga ta ɗauke da jaririya, sai Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Jihar Bauchi (NBA), Bar. Idris Danjuma da Shugabar Sashin Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka (DPP) Bar. Sha’awanatu Yusuf suka amince su bada gudunmawar su domin tallafawa matar ta biyan fansar ta daga gidan gyaran halin, bisa neman shawara Mai Shari’a Rabi Talatu Umar da nufin biya wa matar bashin, nan take kuwa wasu Alkalai biyu da ke duba kotuna, Bala Yunusa da Umar Alkali suka bayar da ta su gudummowar ta naira dubu talatin.
Haka kuma Babbar Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ta cika sauran kuɗin naira dubu arba’in da biyar (₦45000) baya ga kason da shugaban kungiyar Lauyoyin suka bada.”Mun yi haka ne saboda tausayi da kuma duba da ƙoƙarin matar na biyan kuɗin duk da aikin wankau da take yi amma ta gaza biyan kuɗin”. Inji Alkalami.
A Iya Karanta Wanna:Najeriya ta Samu Tallafin Yuro Miliyan 18 daga EU da Ƙasar Jamus
Ganin wanna yunkuri ya sa sauran Alkalai da ‘Yan sanda da Rijistarori suma suka sanya hannu a gidauniyar inda suka bada nasu tallafin. Daga bisani baya ga biyan bashin sai da aka samu rarar naira dubu talatin da shida (₦36,000) kuma aka bawa matar domin ta ja jari tare da addu’ar kare faruwar hakan a gaba.
Read also: NASIR EL-RUFAI YA NEMI AFUWA KAN KARAR DA ICPC TA SHIGAR A KANSA
Kuma sun gargade ta da ta nisanci karbar kayan mutane don yin kasuwanci saboda gudun sake shiga irin wannan matsalar.




























