Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Bulla A Nijeriya
……Hukumar Sojin Nijeriya sun tabbatar da bullar sabbin ‘yan ta’adar
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Wata sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’adda mai suna (Lakurawa), ta bayyana a ƙauyukan Raka, Gwadabawa da Wurno a ƙaramar hukumar Tangaza dake jihohin Sokoto da Kebbi a Nijeriya.
‘Yan ta’addan da akewa laƙabi da (Lakurawa) ana zargin sun fito ne daga ƙasashen Mali da Libya da kuma Nijar inda suke zaune a wani daji da ake kira “Tsauni”.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
A Iya Karanta Wanna:Najeriya ta Samu Tallafin Yuro Miliyan 18 daga EU da Ƙasar Jamus
Rahotanni sun ce ana zargin ‘Yan ta’addan suna shiga ƙauyukan jihar ta Sokoto da Kebbi suna baiwa matasa Naira miliyan 1 don su zama mambobin ƙungiyar ta ta’addanci (LAKURAWA), kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Hukumar Sojin Nijeriya sun tabbatar da bullar sabbin ‘yan ta’adar waɗanda suke kai kawo a tsakanin jihohi, kamar yadda Daraktan hulɗa da kafofin yada labarai na Hukumar tsaro ta kasa, Major General Edward Buba ya sanar.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
A Iya Karanta Wanna:Jirgin Sama Dauke Da Jiga-Jigan NNPCL Ya Rikito A Rivers
Edward Buba ya ce bullar ‘yan ta’adan yana da nasaba da rikicin siyasa dake faruwa a kasashen Nijar da Mali wanda kuma suke kwararowa Nijeriya. Ya tabbatar da cewa dakarun sojin Nijeriya na bibiyar duk wani motsi na ƙungiyar kuma a shirye suke a ko da yaushe domin dakile duk wani rashin tsaro da ka iya faruwa domin kare kasa Nijeriya.




























