Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Sama Da Naira Biliyan 16

NDLEA
NDLEA

Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Sama Da Naira ………  

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun samu nasarar dakume miyagun kwayoyi da aka boye a ƙarƙashin takalma da kuma gashin da ake ƙari wa mata, wanda za a tafi da su Amurka da wasu sassan ƙasashen Turai.

kakakin Hukumar ta NDLEA Femi Babafemi, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi ga manema labarai, ya ce jami’an hukumar da ke filin jirgin sama na Murtala Muhammed ne suka kama miyagun kwayoyin.

Za A Iya Karanta Wanna:Jirgin Sama Dauke Da Jiga-Jigan NNPCL Ya Rikito A Rivers

Babafemi, ya ce a ranar 12 ga wannan watan ne dai jami’ansu suka kama kwayar tramadol dubu biyu da dari da sha takwas (2,118), a ƙarƙashin takalma sha uku da za a kai ƙasar Cyprus, a filin jirgin saman Lagos, sannan suka sake kama ƙarin ɗari uku da tamanin (380) a gidan wanda ya tura da sakon me suna Okenwa Kelvin Uchenna da ke Enugu, a ranar 24 ga wannan watan na Oktoba.

Kwayar Tramadol (2,118) da aka boye a cikin ƙasan takalma 13 da za a kai su ƙasar Cyprus an kama su ne a filin jirgin saman Lagos a ranar 12 ga Oktoban 2024 da kuma ƙarin wasu 380 da aka kwato daga gidan wanda ya aiko da su zuwa Lagos, Okenwa Kelvin Uchenna a lokacin wani samame da aka kai gidansa da ke Enugu a ranar Alhamis 24 ga Oktoba. An kuma samu kuɗi Naira dubu ɗari tara da sittin da takwas da ɗari takwas da tamanin (₦968,880)da mota kirar Toyota Avalon daga hannun wanda ake zargin.

Za A Iya Karanta Wanna:IMF Ta Ce Bata Da Hannu A Janye Tallafin Man Fetur A Nijeriya

Haka kuma, jami’an hukumar ta NDLEA sun samu nasarar kama kwayar tramadol miliyan 26 da dubu dari biyu da 50 da kuma kwalaɓen codeine dubu dari biyar da 8, da dari 4, da adadin kuɗinsu ya kai naira miliyan dubu 16 da miliyan ɗari 683 da dubu ɗari 8, a lokacin da suke binciken haɗin gwiwa tsakaninsu da jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro, kan wasu kwantena da ake zarginsu a tashar jiragen ruwa ta Tincan da ke Lagos da kuma Fatakol, a tsakanin ranakun 22 zuwa 23 ga watan nan na Oktoba.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...