Jirgin Sama Dauke Da Jiga-Jigan NNPCL Ya Rikito A …….
Rahotanni sun tabbatar da faduwar wani Jirgin sama mai saukar ungulu a safiyar yau Asabar bayan ya tashi daga sansani soji a birnin Port Harcourt dake jihar jihar Rivers.
Read also: Iftila’i: Yara Biyu Sun Mutu Sakamakon Mamakon Ruwan Sama
Jirgin ana zargin yana dauke da wasu manyan jiga-jigan jami’an hukumar kula da harkokin Kamfanin man fetur na ƙasa Nijeriya (NNPCL).
Manyan jami’an NNPCL an ce su kai kimanin mutane takwas a cikin jirgin mai samfurin Sikorsky SK76 wanda yake da nambar 5NBQG, ya tashi domin zuwa duba wasu rijiyoyin man fetur a yankin a inda jim kadan da tashin sa ya rikito daga sama ya fada cikin ruwa da misalin karfe 11:22 na safiyar yau. Jirgin ya nutse a cikin ruwa har izuwa haɗa wannan rahoton ba’a ganoshi ba.
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Za a Iya Karanta Wanna:IMF Ta Ce Bata Da Hannu A Janye Tallafin Man Fetur A Nijeriya
Daga bisani mai magana da yawun Hukumar NNPCL, Olufemi Soneye ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an gano gawar mutum uku, saura biyar, amma har zuwa yanzu ba’a bayyana sunayen manyan jami’an na NNPC ba.
Mafi yawan yan Nijeriya na zargin Kamfaniin NNPCL na daga cikin ummul-aba’isin jefa al’ummar ta Nijeriya cikin mummunan hali, yanayin da ya haifar da fatara da tashin gwaron zabi na kayan ma’amula na yau-da-kullum ke yi, wanda kuma ya kara haifar da tsadar rayuwa. Hakan ya sanya al’umma komawa ga Allah mahalicci ta addo’in samun ɗauki.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Za a Iya Karanta Wanna:Kamfanin NNPCL Ya Kara Kuɗi Man Fetur Zuwa ₦897 A Kowace Lita
Wannan dai ya kamata ya zama izina ga al’umma baki ɗaya, musamman masu riƙe da madafin iko masu ƙoƙarin tara abin duniya ta ko wace hanya.




























