Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Sojojin Isra’ila sun yi tutsu

Sojojin isra'ila
Sojojin isra'ila

Akalla sojojin Isra’ila130 sun rubuta wasika da ke nuna alamun tutsu ga gwamnatin kasar cewar ba za su ci gaba da yaki ba, muddin  hukumomin kasar ba za su dauki matakin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tun daga ranar 7 ga watan Oktobar bara ba.

 

Gidan Radiyon Faransa ya rawaito cewar sojojin na Isra’ila a wata wasikar da suka rubuta ta ranar 9 ga wannan wata na oktoba, sojojin da wadanda aka kira domin yiwa kasar yaki sun ce sun fahimci gwamnatin kasar ba ta son kawo karshen yakin domin gudanar da zabe.

Karanta wannan:

Rukakken Dandaba Burakita Ya Gamu Da Fushin Jama’a Yana Tsaka Da Kwaccen Waya A Kano

Daya daga cikin sojojin ya ce tun da babu wani ci gaba wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, saboda haka babu dalilin ci gaba da wannan yakin da kasar ke yi.

Sojan ya ce wannan wani matsayi ne da ya dauka na bijirewa gwamnatin kasarsa saboda yadda ta kai matakin karshe na yaudara.

Sojan ya ce da da gaske ake yi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, da tintini anyi nasara, amma ana tsawaita yakin ne domin kin gudanar da zabe, matakin da zai bai wa (firaminista) damar ci gaba da zama a karagar mulki.

Rahotanni sun ce wasikar ta harzuka gwamnati wadda ta dakatar da wasu daga cikin sojojin.

← Back

Thank you for your response. ✨

 

📷 Reuters

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...