NAHCON: Abdullahi Saleh Ya Samu Nasarar Tantance Wa A Majalisar Dattawa Don Zama Shugaban Hukumar
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
Kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kasashen waje ya tantance Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada shi.
Sanata Abubakar Sani Bello, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai lura da harkokin kasashen waje shi ya jagoranci zaman a inda mambobin kwamitin suka amince wa Farfesa Usman Sale ya zama shugaban hukumar ta NAHCON. Tun da fari sai da Sanata Muhammad Adamu Aliero ya gabatar da kudirin tabbatar da Farafesan a matsayin shugaban, a inda Sanata Shehu Buba Umar ya mara masa baya.
Sanata Buba ya bayyana Farfesa Usman a matsayin kwarare gami da gogewar jagoranci, inda ya bayyana shi a matsayin wani jigo wanda zai iya fitar da kitsen daga wuta gami da daukaka matsayin hukumar aikin Hajji ta NAHCON.
“Babu wanda ya fi Farfesa Sale cancantar zama shugaban hukumar ta NAHCON a halin yanzu, idan aka yi la’akari da ilimi da da gogewarsa da kuma kwazonsa gami da aiki da gaskiya da rikon amana,” in ji Sanata Aliero. Ya kuma jaddada cewar nadin Farfesa Usman ba wai ya zo kan lokaci ne kawai ba, har ma da dabarun da za a bi domin samun ci gaba ta fuskar samar da kyakkyawar alkiblar gudanar da aikin Hajji a Najeriya.
A Iya Karanta Wanna:Farafesa Ibrahim Maibushira Ya Zama Shugaban Kungiyar Safinatul-Khair A Kano
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
Hajj Chronicle ta ruwaito cewa Bayan da aka tantance shi, Farfesa Usman ya nuna matukar jin dadinsa ga damar da aka ba shi don hididmtawa alhazan Najeriya da kasa baki daya, inda ya yi alkawarin hada kan dukkan masu ruwa da tsaki a aikin hajji.
“Wannan amana ce da aka dora gami da karramawa gare ni kuma ina fatan yin aiki tare da daukacin ma’aikatan NAHCON domin cika aikin hukumar na samar da ingantaccen ayyuka ga alhazan Najeriya,” inji shi.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan) kwararre ne a fagen ilimi da gudanar da mulki. Ya yi digirin farko a babbar jami’ar Madina, digiri na biyu a fannin ilimin addinin Musulunci daga jami’ar Peshawar da ke Pakistan, sannan ya yi digirin digirgir a fannin ilimin addinin Musulunci daga Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato a Najeriya.
Shehun Malamin ya kasance shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano daga shekarar 2019 zuwa 2023. Farfesa Usman ya rike mukamai daban-daban, ciki har da shugaban tsangayar ilimin dan Adam na Jami’ar Al-Qalam Katsina, sannan kuma ya zama malami mai ziyara aiki a kwalejin jami’ar Al-Wafaq International University dake Ghana. Haka kuma Farfesa Usman ya yi aikin ba da shawara a kan kwamitocin jihohi da dama.
A Iya Karanta Wanna:Rungumar Sana’a Ce Mafita Ga Matasa, In Ji Pharm. Sule
Bisa la’akari da gogewar sa da samun kai a fannonin rayuwa da dama a ciki da wajen kasar nan, nadin Farfesa Usman ana sa ran zai bude wani sabon shafi na shugabanci ingantacce a hukumar NAHCON, wanda ke shirin kawo sabon fata na bullo da sabbin dabaru gani da hada kai da masu ruwa da tsaki a fanin aikin hajji da kuma gudanar da aiki abin koyi bisa la’akari da tarihinsa na nagarta gami da gaskiya da amana, tare da cikakken ilimi da fahimtar yadda ake gudanar da aikin Hajji.
Read also: Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki



























