Karamar Hukumar Ghari Ta Raba Takardun Daukar Aiki Ga Malamai 50
Daga Tasi’u Dalin-Duniya
Read also: An Yi Kira ga Karamar Hukumar Sumaila da ta Samar da Bandaki a Makarantar Liman Yau JASS Sumaila
Kantoman riko na karamar Hukumar Ghari, Hon Dr Sagiru lawan Shuwaki ya raba takardun daukar aikin koyarwa na wucin gadi a karkashin shirin BESDA da gwabnatin Jahar Kano ke amfani da shi dan ciyar da harkar Ilimi gaba.
Shugaban wanda ya baiyana Ilimi da cewar shi ne Kashin bayan ci gaban kowacce rayuwa da Kuma samun kyakkyawan yanayi na kwanciyar hankali ga bil-adama, inda ya taya wadanda suka samu aiki da su kawo sabbin dabarun koyarwa domin dacewa da manufar gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf na farfaɗo da fanin.
Ya ce don haka a watanni baya Gwamna Abba Kabir ya aiwatar da dokar kar ta kwana ga fanin ilimi a jahar Kano gami da kasar takobin na kungiyar da ilimin daga halin ni ‘yasu.
A Karanta Wanna:Al’ummar Unguwar Tarauni Sun Koka Game Da Ambaliyar Ruwa Dake Barazanar Lakume Gidajensu
Dr Sagiru lawan Shuwaki yace “wannan damar da masu karatun shedar Koyarwa ta Kasa NCE suka samu za ta zamo wani ginshiki a garesu na inganta rayuwarsu da ma sauran mutane baki daya.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewar shirin na wucin-gadi zai share musu hanya na basu damar zamantowa ma’aikatan din-din-din bayan sun yi aiki watani tara bisa kwazo da kwarewa, wanda kuma za a rinka basu dan abun hasafi har tsawon wannan lokaci.
Don haka, Dr Lawan Shuwaki ya bukaci su da su maida hankali tare da aiki tukuru domin ceto ilimi daga halin da yake ciki. Haka kuma ya gargadesu dasu kaucewa makara ko fashi a guraran ayyukansu.
Da yake nasa jawabin shugaban sashen Ilimi na karamar Hukumar Ghari, Bashir Sani Ghari ya godewa kokarin gwamnatin Jahar Kano bisa fito da wannan kyakkyawan tsare-tsare na yunkurin magance matsalolin Ilimi dai-dai gwargwado.
Mal Bashir Sani, ya kara mika godiya ta musamman ga shugaban karamar Hukumar Ghari, Dr Sagiru lawan Shuwaki, a kokarinsa na bunkasa harkokin Ilimi a Lungu da sako na karamar Hukumar ta Ghari.
Read also: Hukumar KAROTA Zata Samar Da Motocin Sufuri Ga Ɗaliban Jami’ar Sule Lamido Dake Jigawa
A Karanta Wanna:Shugaba Tinubu Ya Umarci Kamfanin NNPCL Ya Biya Tallafin Man Fetur
Da Suke godiya wasu daga cikin wadanda suka samu gajiyar shirin, Malam Kabiru Mubarak Yandadi da Malama Hafsa Abubakar sun nuna godiyar su tare da aiki tukuru domin bunkasa ilimi a karamar hukumar da Jihar Kano baki daya.




























