Gwamnatin Kano Ta Sassauta Dokar Hana Zirga-Zirga.
Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga zirga da ta sanya sakamakon ayyukan bata gari da sunan zanga-zanga, an sassauta dokar daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na Rana.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Baba Halilu Ɗantiye, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa manema labarai, a daren ranar Asabar, ya ce an sassauta dokar ne domin al’umma su fito su gudanar da harkokin su na yau da kullum, bisa damuwar da aka shiga.
Ya ci gaba da cewa, yanzu mutane suna da damar da zasu fito su gudanar da al’amuran su kamar yadda aka saba a baya, yana mai cewa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya damu matuƙar gaske kan yadda al’ummar jihar suka samu kan su a ciki.
A KARANTA WANNAN:Rungumar Sana’a Ce Mafita Ga Matasa, In Ji Pharm. Sule
Read also: Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
“Gwmanatin jihar Kano tana kuma ƙara jajanta wa al’ummar jihar musamman wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu yayin zanga-zangar lumanar tsadar rayuwa, yana kuma addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su, ya bai wa iyalan su haƙuri, “in ji Kwamishinan”.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fitar ne da yammacin ranar Alhamis 01 ga watan Agustan 2024, bayan da wasu daga cikin matasa suka rikiɗar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwa, zuwa fasa shagunan mutane tare da ɗibar musu kayayyaki da kuma na gwamnati har da barnatar wa.
A KARANTA WANNAN:KNUPDA, ta kaddamar da kwamitin karbar korafi Game da Mallakar Fili da Makamantasu
Read also: Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Wasu matasa ne dai suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwa, da matsalar tsaro a ƙasar nan, domin nusartar da gwamnatin tarayya halin da aka samu kai a ciki, al’amarin da zanga-zangar ta ƙazanta a wasu guraren, ciki har da jihar Kano.




























