Daga Wakilinmu
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama fitaccen mai amfani da shafukan sada zumuntar nan da aka fi sani da G-Fresh wato Al’amen bisa zargin yin Isgilanci wa Al’qurani.
Read also: Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
Babban Daraktan hukumar Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar wa da manema labarai nasarar kama G-Fresh, a wata hira da kafar radio BBC.
Sufi ya ce hukumar ta kama shi bayan jerin gargaɗin da ta yi masa sakamakon abubuwan da yake wallafawa a shafukan sada zumunta.
Karanta wanna:Mahaifi, Ɗa da Wani Mutum Sun Mutu A kokarin Ɗako Wayar Salula Daga Masai
A cewar sa ”Mun kama shi ne bayan tarin gargaɗin da nasiha da muka sha yi masa kan abubuwan na baɗala da rashin kunya da yake wallafawa shafukansa na sada zumunta.”
Read also: Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanonin Dala Food Nig da POP Cola
Sufi ya ce hukumar Hisba za ta gurfanar da matashin a gaban kotu ranar Litinin mai zuwa.
Al’amen G-Fresh dai ya yi fice a shafukan sada zumunta musamman TikTok, inda yake wallafa bidiyoyin da ba su dace ba, lamarin da ya sa hukumar Hisbar ta ce ta yi masa gargadi da nasiha amma bai ɗauka ba.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
A baya dai G-Fresh ya auri Sadiya Haruna (itama ma’abociyar amfani da shafukan sada zumunta na Zamani), amma ba su jima ba, auren ya mutu, lamarim da ya kai su har ga kotun Musulunci.
Anjima ana kai ruwa rana kan batun auren nasu, amma daga ƙarshe G-Fresh ya sauwaƙe wa Sadiya Haruna, bayan ta biyasa diyyar Naira 500,000.




























