Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Mahaifi, Ɗa da Wani Mutum Sun Mutu A kokarin Ɗako Wayar Salula Daga Masai

Kano
Kano

Daga Wakilinmu

Waɗansu mutane guda uku, a jihar Kano sun haɗu da ajalinsu a ƙoƙarin ɗako wayar salula da ta faɗa ramin shadda a inda guda kuma ya samu kansa cikin mawuyacin hali.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ita ta sanar da haka ta hannun mai magana da yawun hukumar, Malam Saminu Abdullahi, ya sanar da haka ga manema labarai a wata sanarwa a jiya Lahadi.

Saminu ya ce magidancin mai shekara 60, Malam Danjuma, wanda aka fi sani da “Black”, da ɗansa, Ibrahim, mai shekara 35, da kuma wani Aminu Gaye, shi ma mai shekara 35, dukka sun mutu yayin da suke kokarin ɗako wayar salula daga ramin masai a Kauyen ‘Yar’Gwanda da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar a kano.

Sai dai ya ce wani Abba Alasan, mai shekara 28, shi ne, wanda aka ceto da ransa daga masan.

Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da safe.
“Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Tsanyawa da misalin karfe 11:00 na safe. daga wani Aminu Yar’gwanda, cewa wasu maza hudu sun makale a cikin ramin bayan gida (Masai).

“Nan da nan muka aika da tawagarmu ta ceto wurin da misalin karfe 11:15 na safe.

“Danjuma na kokarin ɗako wayar da ta faɗa cikin ramin bayan gida sai ya makale. Bayan haka, ɗansa ya bi shi cikin ramin domin ya ceci mahaifinsa, shi ma ya kasa fita.

“Gaye da Alasan ma sun shiga don ceto mutanen biyu kuma su ma suka makale,” in ji shi.

Abdullahi ya ce an ceto mutum ukun farko da aka same su a sume yayin da aka ceto mutum na huɗu da aka tarar da shi da rai.

Ya ce dukkan waɗanda suka mutu ɗin an miƙa su ga ofishin Sufeton ƴan Sanda Iro Lado, dake garin Tsanyawa.

Jami’in hulda da jama’a ya ce rundunar ƴan sandan ta kai waɗanda lamarin ya rutsa da su asibitin na musamman na garin Bichi domin kula da lafiyarsu inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwar mutanen uku da kuma ɗaya da ke raye.
NAN

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...