Gwamnatin jihar Kano, ta maka tsohon
gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar
Ganduje da matarsa Hafsat Umar da
kuma ɗansa Umar Abdullahi Umar da
ƙarin wasu mutane 5 a gaban kotu bisa
tuhume-tuhume guda 8 masu alaƙa da
cin hanci da rashawa da almundahana
da kuma yin sama da faɗi da wasu
makudan kuɗaɗe.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa
hakan na ƙunshe ne ta cikin wata
takardar shigar da ƙara mai dauke da
kwanan watan 3 ga wannan watan da
muke ciki na Afrilu wadda kuma ke
ɗauke da sunan shaidu kan ƙarar.
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Read also: Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka
Wadanda ake ƙarar sun haɗar da
Abdullahi Umar Ganduje da Hafsat
Umar da Abubakar Bawuro da Umar
Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad
sai Lamash Properties Ltd da Safari
Textiles Ltd da Lesage General.



























