Daga Rabiu Sanusi
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata biyama kimanin ɗalibai dubu ashirin da huɗu da ɗari shidda da hamsin da ɗaya(24,651) kudin makaranta daga makarantun gaba da sakandire guda 12 dake fadin ƙasar nan.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Bayanin hakan na zuwa ne daga bakin shugaban hukumar bada tallafin ilimin gaba da sakandire na jihar Kano Alhaji Kabir Haruna Getso a wata zantawa da yayi da manema labarai a ranar Litinin ɗin nan.
Kabir Getso ya ce kasancewar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na da san Al’umma su samu ilimi kuma duba da irin yanayin da ake ciki na ƙunchin rayuwa, ya yi tunanin sake biyama ɗalibai da suka fito daga Jami’o’i da kwalejoji ilimi daban-daban kuɗin makaranta a karo na biyu.
Karanta Wanna:“Da Akwai Alaƙa Ta Kusa Tsakani Ɗabi’ar Mutane Da Ci gaban Ƙasa”,- Dr. Ƙofarmata
Sh:ugaban ya kuma tabbatar ma da al’umma cewa a halin yanzu jami’an hukumar sa suna kan hanyar zuwa jihohin da ɗaliban suke karatu dan tantance su tare da turowa ofishin hukumar tare da haɗa dukkan bayanan da yakamata dan tura ma Gwamna kamar yadda ya bukata.
“Wannan zuwa da jami’an mu zasuyi zai bamu damar gane su wanene yan asalin jihar Kano, sannan musan kowane ɗalibi tare da abin da yake karanta.”
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
“Kuma ina ganin gwamnati tace wannan ne karo na biyu bayan biyan kuɗin makarantar ɗaliban jami’ar Bayero da tayi kwanan baya, dan haka kada iyayen yara su saki jiki dan ganin gwamnati ta biya suce bazasu biyama yaran su kuɗin makaranta ba.
Karanta Wanna: Ɓarayi Sun Wawashe Kayyan Taransifoma Na Sama Da Naira Miliyan Ɗaya Da Rabi A Ɗiso
Gwamnati ta ce kasancewar abubuwan da yawa a halin yanzu, daga wannan karon baza su sake biyama wa su ɗalibai kuɗin makarantar ba, sai dai akwai shirin da Gwamnatin ke yi don shiga lungu da sako na fadin Qasar nan na lalubo dukkan ɗalibai ƴan asalin jihar Kano tare da sa su cikin tsarin biyan su na scholerahip kamar yadda ta saba.
” wannan aikin tantancewar zai ɗauki jami’an hukumar mu kwanaki 3 ne kacal watau daga gobe Talata har zuwa ranar Alhamis sannan a kammala, dan haka dukkan ɗalibin dake karatu a wadannan makaratu guda 12 idan baya makaranta yayi ƙoƙarin komawa.
Shugaban hukumar yace makarantun da za’a tantance ɗaliban sun haɗar da Jami’ar Gwamnatin tarayya dake Dutsin-ma da Jami’ar Marigayi Ummaru Musa da su ke a Katsina sai kwalejin ilimi dake Kano da kwalejin koyar da aikin noma dake Hotoro Karamar Hukumar Taraunin jihar Kano.
Read also: Auren Gata Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne, Inji Sheik Hadi MaiHula
Karanta Wanna: Majalisar Dokokin Jahar Kano Za Ta Gyara Dokar Ƙarin Shekaru 5 Na Aikin Gwamnati
Sauran sun haɗar da Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau, Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi da Jami’ar Sule Lamido Jihar Jigawa da kuma Jami’ar Ahmadu Bello dake Zarian jihar Kaduna tare da Jami’ar Tarayya dake Gombe da Jami’ar Usman Dan fodio dake Sokoto sai kuma Jami’ar jihar Borno.




























