Daga Wakilinmu
Wani Matashi ɗan shekaru 27 mai suna Chinalu Ogbonna, ana zarginsa da hallaka mahaifinsa, Maduka Ogbonna, ya kuma ƙwaƙule idonsa na hagun.
Read also: Babban Yaron Ɗan Ta’adda Bello Turji, Yalo Ɗan Bokolo ya Baƙunci Lahira
Read also: Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
Majiyarmu ta ce abin ya faru ne a ranar Litinin da talatainin dare a gidan su dake daura da ƙaramar Sakandire ta Amuzukwu dake Umuahia a jihar Abia.
Read also: Ambaliya ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
Jaridar Vangurd ta ce har yanzu ba a da cikakiyar dalilin da yasa matashin ya aikata hakan, sai dai matasan da suka kama mai laifin sun ce ya tabbatar musu da aikata hakan bisa buƙatar yin tsafi da idon mahaifin nasa.
Majiyar ta ce ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sanda, na jihar Abia Kwand, ASP Maureen Chinaka, amma ba a same shi a waya ba, kuma anbar masa saƙon kar-ta-kwan bai bada amasa ba har yuzuwa haɗa rahoton.



























