Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Majalisar Dokokin Jahar Kano Za Ta Gyara Dokar Ƙarin Shekaru 5 Na Aikin Gwamnati

Majalisar Kano
Majalisar Kano

Daga Wakilinmu

Majalisar Dokokin jahar Kano ta ce za ta gyara dokar ƙarin shekaru 5 na aiki gwamnati da ‘Ritaya da tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta yi.

Da yake gabatar da ƙudirin hadin guiwa na gaggawa akan batun, shugaban masu rinjaye kuma wakilin ƙaramar hukumar Dala Alh. Lawan Hussaini Chediyar Ƴan Gurasa ya ce gyaran dokar zai baiwa matasa masu hazaƙa damar ba da ta su gudummawar wajen ci gaban jahar kano.

Ka karanta:Ƙungiya ta Gargadi Majalisar Kano kan Rushe Sabbin Masarautu

Ya ce za su dawo da dokar domin yi mata kwaskwarima ta yanda wa’adin aikin gwamnati zai koma shekaru 35 a yayin da lokacin ritaya zai koma shekaru 60.

Shugaban masu rinjayen ya ƙara da cewa gurbin manyan ma’aikatan zai iya samarwa matasa Dubu Goma Sha Biyu aiki, don haka da akwai buƙatar a kalli dokar domin sabuntata ta yadda za a bada damar bawa matasa masu jini ajika dama.

Ka karanta:“Mun Gamsu Bisa Nadin Bashir Diso A Matsayin Akawun Majalisa,” In ji Shugaban Safina

Alh. Lawan Hussaini Chediyar Gurasa ya bayyana cewa a yanzu haka akwai Dubban matasa masu Difiloma da NCE da Digiri na biyu da na uku amma ba su da aiki wadda hakan ya zaman dole a ba su dama.

Idan za a tuna gwamnatin da ta gabata ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ita ta gyara dokar ɗaukar aiki da yin ritaya ga ma’aikatan jihar, inda ta ƙara shekaru 5 akan shekarun haihuwa da na ritaya, saboda ƙarancin kuɗin biyan waɗanda suka bar aiki wato garatuti.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...