Minista Ata Ya Amshi Bakuncin Tsohon kakakin Majalisar Zamfara, Ya Yabawa..
Daga SA K/Na’isa
Read also: Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli
Ƙaramin Ministan ƙasa a ma’aikatar Gidaje da raya Birane, Rt. Hon. Yusif Abdullahi Ata ya amshi bakuncin tsohon Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Zamfara, Rt. Hon. Sunusi Rikiji da kuma tsohon kwamishina na jihar Zamfara Hon. Kabiru Mori Birnin Magaji.
A ziyarar taya murna da manyan jami’an na jihar Zamfara suka kawowa Minista Rt. Hon. Ata sunyi addu’a da fatan alheri ga Ministan kasa a ma’aikatar gidaje da raya birane Rt. Hon. Yusif Abdullahi Ata, domin Allah ya taya shi riko.
Har ila yau, Minista Rt. Hon. Yusif Abdullahi Ata yakai ziyara shelkwatar karbar korafe-korafe ta tarayya ( Public Complaints Commission), dake birni tarayya Abuja inda ya gana da Babban kwamishinan hukumar na kasa Alh Bashir Abubakar.
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU

PCC
A Iya Karanta Wanna:Alkalai Sun Yi Gidauniya Domin Kubutar Da Matar Aure Dake Tsare A Gidan Yari
Hon. Minista Ata da Kwamishina Abubakar sun gana da junansu, kasancewar wannan hukuma ta karbar korafe-korafe ta tarayya itace hukumar da Rt. Hon Ata yayi aiki kasa da mako biyu kafin likkafarsa tayi sama zuwa mukamin Ƙaramin Ministan kasa a Ma’aikatar Gidaje da raya Birane.
Yayin da yake zantawa da wakiliyar tashar ta talabijin ta Ombudsman mallakin hukumar ta karbar korafe-korafe Minista Yusif Abdullahi Ata yace ” a kasa da mako biyu da nayi aiki da hukumar, naji daɗin gudanar da alakar aiki mai armashi da ɗaukacin ma’aikatan ofishin hukumar na Kano.
Read also: Hukumar NDLEA ta Gano Maboyar Miyagun Kwayoyi a Ƙarƙashin Ƙasa a Kano
A Iya Karanta Wanna:Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Bulla A Nijeriya
Mun samu wannan labarin daga Mataimaki na musamman ga minista a fanin kafafen sadarwa, Adamu Aminu Fagge.




























