Daga Wakilinmu
A wani muhimmin mataki na ƙarfafa hanyoyin sadarwa na kiwon lafiyar jama’a, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kano Baba Halilu Ɗantiye ya gudanar da wani muhimmin taro a ranar Litinin tare da wata tawaga daga Ma’aikatar Lafiya ta jihar.
Read also: Kwararriyar Mai Karanta Labarai Lami Maccido Ta Rasu Tana da Shekara 72
Kwamishinan ya bayyana cewa taron ya ta’allaƙa ne kan buƙatar da ta zama wajibi a haɗa kai ba tare da samun matsala ba tsakanin jami’an yaɗa labarai a dukkanin ƙananan hukumomi 44 da jami’an kiwon lafiya daga ƙananan hukumomi da kuma ma’aikatar lafiya ta jiha.
Ɗantiye ya jaddada buƙatar samun haɗin kai a tsakanin ɓangarorin biyu wajen tabbatar da samun afkuwar annoba tare da samun sahihan bayyanai kafin a sanar wa al’umma.
“Tabbatar da lafiyar jama’a da kare lafiyarsu na buƙatar haɗa ƙarfi-da-ƙarfe daga ɓangaren yaɗa labarai da ɓangaren lafiya”, Dantiye ya faɗa. Ya ƙara da cewa “Ta yin aiki da juna ne kawai zai ba mu tabbacin samun sahihan bayanai na samun ɓarkewar annoba ko akasin haka. Haka kuma zai taimaka ƙwarai domin faɗakar da al’umma don ɗaukar matakan kariya da suka dace cikin hanzari”.
Ɗantiye, wanda ya ba da tabbacin goyon bayan ma’aikatar yaɗa labarai don cimma manufofin da ake so, ya bayyana cewa taron ya zama wani dandamali don gano dabarun inganta hanyoyin sadarwa tsakanin jami’an yaɗa labarai da jami’an kiwon lafiya a matakan ƙananan hukumomi da jihohi.
A nasa jawabin, jagoran tawagar na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Dakta Ibrahim Aliyu Gano wanda kuma shi ne Mataimakin Darakta mai kuɗa da Ma’aikata da Horarwa kuma mai kula da cutar Tarin Fuka da Kuturta a ma’aikatar lafiya, ya bayyana ƙudurinsu na inganta haɗin gwiwa da haɗin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki da ke da alaƙa da lafiyar jama’a da kuma yaɗa labarai.
Dr. Gano ya tabbatar da ƙwazon da ma’aikatar lafiya ta yi wajen tallafa wa tsare-tsaren da ke inganta hada-hadar yaɗa bayanai ba tare da matsala ba da kuma ƙoƙarin kula da lafiyar jama’a a matakin farko.
A wani labari mai kama da wannan, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya kuma karbi wata tawaga daga UNICEF ƙarƙashin jagorancin Ogu S. Makiya, Ƙwararren wajen sauya ɗabi’un jama’a na UNICEF a ofishinta Kano.
Read also: Bashi Ko Ceton Rai? Kukan zuci da Siraɗin da Ma’aikatan Gwamnati ke ciki a Nigeria
Enemaku ya ce sun kai ziyarar ne domin sabunta manufa da kuma aniyar ƙara samun haɗin kai tsakanin ma’aikatar yaɗa labarai da UNICEF, tare da bayar da haɗin kai ga kiyaye lafiyar al’umma da kuma inganta sahihan bayanai da kuma abin dogaro.
Darkta Ayyuka na musamman na Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano, Sani Abba Yola ne ya sanar da manema labarai haka ciki har da kafar sadarwa ta The STENTORNES.




























