Daga Wakilinmu
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano sun gudanar da gaggarimin taro karo na farko bayan zaɓen shekara ta 2023 da ya gabata a Club Road Kano.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Taron wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata ya samu jagorancin ɗan takarar Gwamna na jam’iyyar a zaben 2023, Alh. Saddiq Aminu Wali ya kuma samu halartar sauran tsofafin ƴan jam’iyyar a matakin majalisar dattawa, da ta wakilai da kuma ƴan majalisar dokoki ta jiha.
Wali, ya ce taron an kira shi ne domin yin tunani a kan yadda jam’iyyar ke gudanar da ayyukanta da kuma dabaru wajen jawo hankalin al’ummomin da ke sha’awar jam’iyyar gami da yabawa ƴaƴen jamiyyar bisa juriya da ƙaunar juna.
Ya lura cewa akwai yiwuwar jam’iyyar ta sake zama mai karfi kuma ta ci zabe, idan akai la’akari da yadda sauran jamiyyu ke taka rawarsu ta fuskar gudanar da mulki a ƙasa da sauran jihohi dake faɗin tarayyar Najeriya.
Wali ya faɗa cewa mutane da yawa sun cimma burinsu ta amfani da dandalin jam’iyya saboda al’ummarta sun karkace daga kan aƙida da shirye-shiryen da ba a wasu bangarori.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Saddiq wanda ya yi magana ta bakin tsohon shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Muhammina Bako Lamido ya jinjina wa mambobin jamiyyar bisa hakuri da juriya da kuma dagewa akan abin da suka sanya gaba.
Ya kuma roƙi mambobin su fara shirin gangami tare da zaburar da sauran ƴaƴen jamiyyar domin farkawa daga baci a dukkani saƙo da lungu a jihar nan.
Ya ce nan ba da jimawa ba zai fara ziyarar cikin gida don karɓar sabbin mambobi a cikin jam’iyyar tare da sabunta katin jam’iyya.
Haka kuma ya bayyana aniyar jam’iyyar na shiga zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe a jihar nan, idan har hukumar zaɓen jihar ta samar da kyakyawan dandali da kuma daidaito a tsakanin jam’iyyu.
A jawabinsa Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Saddiq Wali, Alhaji Aminu Labaran Baba ya ce yanzu abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne sanya jagorori masu ƙarfi a dukkan matakai waɗanda za su samu amincewar ga dukkan mambobi tare da jan hankalin wasu sabbin mambobi waɗanda ke da muradin shigowar sabuwar PDP a jihar Kano.
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Da take jawabi, ƴar takarar majalisar dokokin jiha a zaɓen da ya gabata daga mazaɓar Dawakin Tofa, Hajiya Lubasatu Ibrahim Tunfafi, ta shawarci dattawa da su zaɓi shugabanni jam’iyyar bisa cancanta musamman matasa domin ci gaban jam’iyyar a dukkan matakai.
Sauran wadanda suka yi jawabai sun haɗar da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Jihar Kano, Bello Ado Yandaɗi da Shugaban Ƙungiyar ƴan takara na Jam’iyyar PDP Hon. Muzakkir Rabi’u da ɗan takarar jam’iyyar a matakin majalissr wkili da ke wakiltar mazabar Wudil/Garko, Hon.Dagumawa da Kwamared Aminu Sa’ad Beli, shugaban ƙungiyar ƴan takarar majalisar jiha, kuma mai wakiltar ƙaramar hukumar Rogo da kuma shugabar mata ta jam’iyyar a matakin jiha, Hajiya Aisha Musa Tarauni da sauran manyan mutane.




























