Daga Wakilinmu
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce Kuskure ne hukumomi su riƙa kamo matasa maza da mata suna jefa wa a cikin mota wai a matsayin gyara.
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Gwamnan yayi wannan jawabin ne a yau Litinin yayin da yake ganawa da malaman Addinin Musulunci a fadar gwamnatin Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce wannan bai yi dai-dai da addini ba, “yadda na ga wani bidiyo da yake yawo a kafafen sadarwa, yadda hukuma Hizba taje wani waje a faɗin kano harma da wajen da ɗalibai suke a zaune domin kama su, inda a yayin kamen akayi abin da bai dace ba da tsari na addini.”
Ka Karanta Wanna:Ɗan Shekara 27 Ya Hallaka Mahaifinsa Ya Kuma Ƙwaƙule Idonsa Na Hagun
“Adan haka dole gwamnati tayi duba akan wannan abun da kuma samar da tsari wanda zai samarwa da aľ’umma musamman matasa tarbiya.” Inji Gwamna.
Gwamnan ya kuma ce yin wa’azi da addu’a shine mafita ga wanda ake ganin ba ya kan tarbiya da kuma aikata rashin dai-dai, ba a aibata shi ba, ya ce malamai faɗakarwa ce tasu ga al’umma.
Haka kuma Gwamna, ya yi albishir ga kanawa cewa a wannan lokaci na karatowar azumin watan Ramadan gwamnatin sa ta yiwa al’ummar jihar Kano tanadin raba abinci domin rage matsin rayuwa da ake ciki.
Ka Karanta Wanna:Majalisar Dokokin Jahar Kano Za Ta Gyara Dokar Ƙarin Shekaru 5 Na Aikin Gwamnati
Majiyarmu ta ruwaito Gwamna ya bada tabbacin gyaran duk wasu masallatan juma’a da suke faɗin jihar nan, la’akari da yadda wasu masallatan suka lalace babu ƙyan gani.
Read also: Gwamnan Abba Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin 2026, na zambar N1.368 tiriliyan
Ka Karanta Wanna:DA ƊUMINSA: Har Yanzu Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Shine Kwamanda Hisbah A Kano, Inji Hukumar
Haka kuma yayi alwashin zai ƙarawa dukkanin limaman masallatan juma’a kuɗaɗen da ake biyan su na wata da kuma basu tabbacin kuɗin zai dunga zuwa kai tsaye daga ofishin babban Akanta na jiha domin tabbatar da daidaito da kaucewa kuskunda.




























